Toh : Jibrin ya karasa hedkwatan DSS
Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisan wakilai ta kasa ,Abdulmumini Jibrin ya kai karan kakakin majalisa Yakubu Dogara hedkwatan hukumar DSS da ke Abuja. Ku tuna cewan Abdulmumini Jibrin yace zai kai karan kakakin majalisa hukumomin yaki da rashawa da yan sanda. Jibrin ya bayyana hakan ne a safiyar yau ,litinin, 1 ga watan Agusta .
Abdulmumin Jibrin
Tsohon shugaban kwamitin ya kai ofishin DSS misalin krafe 12.49 a yau. A yanzu haka yana cikin ofishin shugaban hukumar DSS ,Lawal Daura domin shirya kara akan kakakin majalisan wakilai yakubu dogara. Abdulmumin Jibrin at the DSS office on Monday, August 01, 2016.
Kafin yau, Jibrin ya fito da zargi akan Dogara da mataimakin kakakin majalisa Hon, Yusuf Lasun Suleiman,da Alhassan Doguwa ,da shugaban marasa rinjaye ,Leo Ogor da wasu mambobin majalisa 9.
KU KARANTA : An kai karar majalisa kan arigizon kasafin kudi
Da safiyar nan, jibrin ya je ofishin hukumar yaki da rashawa da laifuffuka mai kama da haka mai zaman kanta ICPC ,inda ya kai karan kakakin majalisa. Yayi tuhuman cewa Dogara da wasu shugabannin sunyi kari cikin kasafin kudin kasa kimanin kudi N40 biliyan don aljihun kansu.
A ofishin ICPC , Jibrin ya fada ma jaridar NAIJ.com cewa yana sa ran a gudanar da bincike na gaggawa akan al’amarin.
The post Toh : Jibrin ya karasa hedkwatan DSS appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.