Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Jami’an tsaro sun yiwa Warri tsinke kan tarzomar tsageru

0

-Rundunonin jami’an tsaro na kasar nan sun yiwa garin Warri na Jihar Delta tsinke

-Mai ba shugaba kasa shawara kan shirin afuwa da ajiye makamai na tsaffin mayakan, ya ce a kwantar da hankali

Wasu jami’an tsaro a bakin aiki a yankin Niger Delta

Sakamakon wasu bayanai na sirri dangane da  shirin da wasu tsaffin tsagerun Niger Delta na yin bore kan rashin biyan su alawus-alawus na wata-wata, jami’an sojin ruwa da na kasa da na ‘yan sanda da kuma jam’an tsaro na farin kaya sun yiwa ga Warri tsinke.

A cewar jaridar Vanguard, jami’an tsaron wadanda aka girke su a wadansu muhimman wurare daban-daban a garin, sun kuduri aniyar wargaza duk wani taron zanga-zanga ba bisa ka’ida ba na tsaffin tsagerun.

KU KARANTA: Sojoji sun soma luguden wuta a kan tsageru

Mai ba shugaban kasa shawara kan ayyukan da suka shafi yankin Naiger Delta, kuma mai kula da shirin afuwa ga mayakan, Brigediya Janar Paul Boroh mai ritaya ya ce , babu wani dalilin da zai sa a tsaffin mayakan su yi zanga-zanga domin “Da akwai basussuka da suke bi, amma yanzu kudi ya samu, kuma babban bankin Najeriya zai soma turo da kadaden a yau ko gobe, na kuma sanar da tsaffin mayakan hakan, sai dai ban san dalilin da ya sa wasu suka dage sai sun yi zanga-zanga ba.”

Jaridar ta ci gaba da cewa, Wata majiya daga jam’an tsaro na farin kaya DSS ta ce tsafffin mayakn sun shirya yin zanga-zanga ne a ranar Laraba da kuma Alhamis  amma kuma jami’a tsaron suka wargaza aniyarsu.

The post Jami’an tsaro sun yiwa Warri tsinke kan tarzomar tsageru appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса