Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa
A yau ne, 3 ga watan Agusta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kawo ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara fadar shugaban kasa .
Mai daukan hoton shugaban kasa , Bayo Omoboriowo ne ya watsa a shafin sada zumuntansa ta instagram, yace an yi ganawar ne a sirrance. Jonathan ya iso fadar shugaban kasa ne a wata mota Range Rover marked KWL 86 CN kuma daya daga cikin ma’aikatan Buhari ne ya tarbe sa .
Labarai sun fara fitowa akan makasudin ziyarar da tsohon shugaba Jonathan ya kawo ma buhari ; gas su nan
- Hayagagan Neja Delta
Tsohon shugaban kasa Jonathan ya zo tofa albarkacin bakinsa akan hayaniyar da ke faruwa a yankin Neja Delta da kuma yadda abubuwan da ke faruwa na fashe-fashen bututun mai da ke durkusar da tattalin arzikin kasa.
Kungiyar tsagerun neja delta sun durkusar da tattalin arzikin Najeriya
- Tattalin arzikin kasa
Karkashin jagorancin shugaba jonathan,Tattalin arzikin kasan najeriya tanada armashi fiye da yadda take karkashin Gwamnatin Buhari.
- Yaki da cinhanci da rashawa
Abinda shugaba Buhari yayi amfani da shi wajen yakin neman zabe shine cewan zai yi yaki da rashawa . kuma bayan ya lashe zaben ,ya damke abokan aikin Jonathan da dama.
KU KARANTA : Ya mutum bayan hawa palwayan wuta a taron siyasa
The post Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.