Makiyaya sun kashe mutane 26 a jihar Kaduna, Adamawa
-Rahoton ya nuna cewa adadi wadanda aka ce sun mutu da wadanda suka bata suna iya fin haka yawa saboda har yanzu kauyukan da abun ya shafa suna cikin halin juyayi
-Lumsan Dilli, wani wakilin yankin, yace da yawa daga wadanda aka ayyana ba’a gani ba sun mutu, yayinda makiyaya suke ci gaba da kisan kai, da kuma kona kauyuka
-Rahoton ya bayyana cewa an kashe mazaje shidda (6) da kuma mata uku (3) a Gada Biyu, yayinda aka kashe mazaje biyu (2) a Akwa’a cikin jihar Kaduna
makiyayi da bindiga
Yan bindiga da aka yarda cewa makiyaya ne sun kai hari kauyuka a jihar Adamawa da kuma jihar Kaduna, sun kashe a kalla mutane 26 sun kuma ji wa mazauna da dama raunuka.
Wasu da dama kuma sun bata a hare-haren guda biyu jaridar Vanguard ta ruwaito.
Rahoton ya nuna cewa mutane 15 ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai kauyen Kodomun da kewayenta cikin karamar hukumar Demsa dake jihar Adamawa, yayinda aka yanka mutane 11 a kauyuka uku kusa da garin Godogo, karamar hukumar Jema’a dake jihar Kaduna.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya na shirin horar da yan boko haram 800
An ruwaito cewa mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Mr Martins Babale; Brigadiya-Janar Benson Akiroluyo, da kuma Mohammed Ghazzali, kwamishinan yan sanda na jihar, sun kai ziyara kauyukan a ranar Talata, 2 ga watan Augusta na shekara 2016, domin ganin yanda lamarin yake.
Sun kuma kai ziyara ga masarautar Batta, Hamman Batta, Cif Alhamdu Teneke, domin taya shi jajen kan abunda ya faru.
Wanda ke wakiltan Demsa a majalisar jihar, Mr Lumsan Dilli ya bayyana cewa adadin mutane da aka ce sun mutu suna iya fin haka. Yace dayawa daga cikin wadanda aka ce sun bata ana ganin sun mutu, yayinda makiyaya suka ci gaba da kisan kai, da kuma kona kauyuka a yayinda suke ci gaba da tafiya.
Ya mukaci a saka tsaro a kauyukan da abun ya shafa da sauran kauyuka saboda gudun sabon hari.
The post Makiyaya sun kashe mutane 26 a jihar Kaduna, Adamawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.