Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Fayose ya saukewa iyayen marayu garar alheri (hotuna)

0

-Gwamnan jihar Ekiti ya saukewa wasu taron mata garar kayyakun masarufi

-Ya yi alkawarin ci gaba da ta rarraba kayayyakin masarufi ga talakawan jihar

-Gwamnan ya yi alkawarin bayar da tallafin N5000 ga mata 10,000

Gwamna Fayose ya yi alkawarin ci gaba da rarraba kayayyakin masarufi ga talakawan jihar, gwamnan ya jaddada hakan ne a hirarsa da ‘yan jaridu bayan da ya yi wani taro da kungiyar matan da mazajensu suka rasu wadanda suka fito daga sassan jihar.

KU KARANTA: ⁠⁠⁠Ina bayan Modu Shariff sai dai… –Fayose

Gwamnan ya yi taron da ne da matan a cibiyar kula da cigaban mata ta Funmilayo Olayinka da ke Ado Ekiti a ranar Talata.

KU KARANTA: Tirkashi: An yanka ta tashi a jihar Ekiti

Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da taimakawa matan tare da faranta musu, ya kuma yi musu alkawarin rabon su a shirinsa na rage talauci a jihar a inda za a ba masu cin gajiyar shirin su 10,000 Naira 5,000.

Kowacce daga cikin mahalartar taron ta tafi gida da kayan abinci da wasu ‘yan kudi, sannan, bayan sun yiwa gwamnan addu’a da fatan alheri, sun bukaci gwamnan da ya ci gaba da taimaka musu.

Gwamna Fayose na shan suka dangane da yadda ya ke rarraba kayakin masarufi ga ‘yan jihar a yayin da  ya yi watsi da muhimman ayyukan ci gaban jihar a cewar wasu masu sharhi. A kwanakin baya, Fayose ya fuskanci zanga-zanga a jihar bayan da hukumar EFCC ta bankado wata badakala ta miliyoyin nairori da kuma mallakar wasu gidaje na alfarama da gwamnan ya yi a Abuja da kuma Lagos, wanda hukumar ta ce ba halak ba ne.

 

The post Fayose ya saukewa iyayen marayu garar alheri (hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса