An daure shi kan laifin satan lemun kwalba
An yanke ma wani mutum dauri a gidan yari saboda kama shi da akayi da laifin satan katan din lemun kwalba, Maltina.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, an daure mutumin ne mai shekaru 23 mai suna Hnery Okeke da laifin sata. Daurin da aka yanke ma Okeke na tsawon watanni shidda ne, bayan kama shi da laifin satan kwali biyu na lemun kwalba Maltina hade da babur wanda kudinsa ya kai naira 155,000 da kotun majistre ta Ikeja tayi.
A lokacin da yake yanke hukunci, Alkali O.A Olayinka ya hana ma mai laifin daman biyan tara, inda yace “mai lafin zai yi zaman gidan kaso na kirikiri don hakan ya zama izna ga sauran mutane”. Okeke ya aikata laifin ne da misalign karfe 4 na asuba a ranar 13 ga watan yulio a layin Mafoluku dake yankin Oshodi, jihar Legas.
A lokacin da ya bayyana a gaban kotu, mai shigar da kara Sajan Donjor Perezi yace “mai laifin ya daure kwalayen Maltinan ne a kan mashin, kuma yana kokarin tserewa kenan aka kama shi.
The post An daure shi kan laifin satan lemun kwalba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.