Ogenyi Onazi ya koma buga kwallo a kasar Turkiyya daga Italy
Shahararren dan wasan kwallon kasar Najeriya da tsakiya watau Ogenyi Eddy Onazi ya bar kungiyarsa ta SS Lazio dake kasar Italiya ya zuwa kungiyar Trabzonspor dake kasar Turkey har ta tsawon shekaru 5.
Shi dai dan kwallon Onazi ya shafe shekaru 5 a tsohon kulob din nasa kafin ya koma Trabzonspor yanzu. A da can dai dan kwallon yana taka leda ne a wata kungiyar kwallo ta T. B Joshua mai suna My People FC a nan gida Najeriya.
An dai ruwaito cewa kungiyoyin kwallo kamar su Arsenal da Liverpool har da ma Tottenham sun nuna sha’awar su wajen siyen dan wasan amma sai ya zabi ya tafi kasar Turkiyya din. Kamfanin jaridar Premium Times da kuma na La Repubblica na kasar Italiya sune suka ruwaito cewar an kammala yarjejeniya tsakanin dan wasan Onazi da kuma sabuwar kungiyar tasa makwanni da dama da suka wuce amma saboda rashin zaman lafiya musamman ma na diflomasiyya dake a kasar ta Turkiyya shine ya sa aka jinkirtar da cinikayyar.
An dai ruwauto cewa dan wasan ya koma sabuwar kungiyar sa ne a kan kudi kimanin N1.8b wanda yayi dai dai da €5. Wasun yan kasar Najeriya da suke buga kwallo a kasar ta Turkiyya sun hada da Emmanuel Emenike, Godfrey Oboabona dama Kenneth Omeruo.
The post Ogenyi Onazi ya koma buga kwallo a kasar Turkiyya daga Italy appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.