Kungiyar ISIS sun nada sabon shugaban Boko Haram
Kungiyar nan mai ikirarin kafa daular musulunci dake a yankin kasar Syria watau The Islamic State (IS) sun bayyana cewar sun nada wa kungiyar Boko Haram ta kasar Najeriya wani sabon shugaba.
Kungiyar ta ISIS din dai ta bayyana sabon shugaban ne da suna Abu Musab Al-Barnawi wanda shine mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram da baya. Shi dai Al-Barnawi ya dare kujerar shugabancin kungiyar na Boko Haram tun bayan wasu rahotanni da ke nuni da cewar an kashe tsohon shugaban na Boko Haram wata Abubakar Shekau. An dai samu wannan labarin ne daga wata sabuwar mujalla da kungiyar ta ISIS ke fitar wa duk karshen wata. Ku saurari cikakken bayani nan gaba…
The post Kungiyar ISIS sun nada sabon shugaban Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.