EFCC ta kwace gidajen Fayose a Abuja da Lagos
-Rigar kariyar Fayose ba za ta hana kwace kadarorinsa ba a cewar wata Kotun Tarayya
-Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya sabunta umarninsa na farko kan kadarorin gwamnan
-Lallai EFCC ta kammala binciken ta kwanakin 45
Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti
A ranar Talata 2 ga watan Agusta ne Mai shari’a Dimgba Nnamdi na babban kotun tarayya a Abuja ya jaddada umarnin da ya bayar a ranar 20 ga watan Yuli shekara ta 2016 ga hukumar EFCC na kwace gidajen gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, har sai ta kammala bincike.
A yayin da ya ke yanke hukunci jim kadan bayan sauraren rokon da lauyan Fayose Cif Mike Ozekhome SAN ya shigar, a inda ya ke rokon kotun da ta kau da umarnin a bisa wasu hujjoji guda 10, mai shari’a ya ce bai yi karan tsaye ga sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasar nan ba na 1999 wanda ya sa wa gwamnan rigar kariya daga kowanne irin tuhume-tuhume sai dai, a cewarsa, ”……hakan ba za ‘a fassara shi da cewa tsaiko ne ga yaki da cin hanci da rashawa ba. Ma’ana, hukumar EFCC da sauran masu aiki irn na ta, ba za su leka a irin kadarori da asusun ajiyar wani gwamna mai ci ba…”.
KU KARANTA: Tirkashi: An yanka ta tashi a jihar Ekiti
Mai shari’a Dimgba ya ce umarnin Kotu na kwace kadarorin gwaman na 20 ga watan Yuli, na da kwanaki 45 na aiki daga ranar da aka bayar da shi, wanda a cikin wadannan kwanaki ne hukumar za ta kammala dukkanin binciken ta.
Kadarorin da umarnin ya shafa wasu gidaje ne guda hudu, masu dakuna hudu-hudu a rukunin gidajen alfarma na Victoria Island a jihar Lagos, da kuma wasu gidaje biyu a lamba 44 Osun Crescent da 1504 a unguwar Maitama a Abuja, hukumar EFCC na zargin gwamnan da mallaki gidajen ta hanyar kashe-mu-raba da ‘yan kwangila da kuma, wasu hanyoyin da ban a halak ba.
The post EFCC ta kwace gidajen Fayose a Abuja da Lagos appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.