Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Sojoji sun fattaki tsageru daga bututun mai a Arepo

0

-Rundunar sojojin killace yankin Areppo domin cafke tsageru Niger Delta

-Luguden bama-bamai daga jiragen saman yaki ya kassara tsagerun a jihar Ogun

-Sojin sun sha alwashin ganin bayan tsagerun

rundunar sojojin sama

Bayan da jiragen sama na rundunar sojin Najeriya suka yi ruwan bama-bamai a kan tsagerun Niger Delta Avengers, tsagerun sun tsere daga Arepo. A wani rahoton jaridar Punch, ta ce wasu kananan jiragen ruwan yaki na musamman na rundunar sojin ruwan kasar, suka jagoranci kai hari a kan tsagerun, kari a kan laguden da suka sha ta sama a yankin har na kwanaki biyar.

KU KARANTA: ‘Yan sanda da tsageru na cigaba da barin wuta a Lagos

Rahotanni  na cewa sojin ruwan ba su gamu da wata tirjiya ba a lokacin da jiragen suka kutsa yankin da tsagerun suke cin Karen su babu babbaka, suna barin wuta, yankin da ake zargin cewa nan ne dandazon  tsagerun inda suka yi ajalin jami’an tsaro da yawa a baya.

Kakakin shalkwatar tsaro ta kasar Brigediya-Janar Rabe Abubakar, ya tabbatar da labarin, sannan ya kuma ce, gamayyar rudunar sojin kasar ta soma kai hari ta kasa a kan tsagerun, ya kuma kara da cewa, ba za su saurara ba har sai sun raba tsagerun da hanyoyin butun man kasar a Arepo.

Abubakar ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin tsagerun sun gudu zuwa tsibirin Tongeji da ge kusa da  Badagry a inda ake ce nan suke sake taruwa, haka na kuma in ji shi, wasu tsagerun sun tsere zuwa tsibirin snake, nan ma, a cewarsa, sojin na Najeriya, za su bi sawun su.

 

The post Sojoji sun fattaki tsageru daga bututun mai a Arepo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса