Yan bindiga sunyi garkuwa da malamin Jami’a
Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun sace wani malamin Jami’ar tarayya dake garin fatakwal Dakta Reginald Ohiri.
A ranar 1 ga watan agusta ne yan bindigar suka kutsa kai cikin gidan malamin da karfi da yaji suka tafi dashi, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, yan bindigan sun tuntubi iyalan malamin inda suka bukaci a basu miliyan 2 kafin su sake shi. Majiyar mu ta fada mana cewa an sace Ohiri ne a gidansa dake unguwar Aluu a karamar hukumar Ikwerre.
Jami’i mai magana da yawun hukumar jami’ar Dakta William Wodi ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya ce bai san takamaiman lokacin da aka sace malamin ba. Wodi yace “na samu labarin haka. Sunan shi Dr Ohiri kuma malami ne a tsangayar karatun ilimin sinadarai a jami’ar fatakwal. Ina da labarin an sace shi ne a gidansa dake garin Aluu.”
Nnamdi Omoni mai magana da yawun hukumar yansandan jihar Ribas yace an kira shi an bashi labarin afkuwar lamarin, amma yace ba’a zayyana mai gaba daya labarin ba. Jami’in yansandan ya ce hukumar yansada zata fara bincike akan lamarin.
A kwanakin baya ne kotun jihar Delta ta yanke ma wani kasurgumin barawo Kennedy Itoje daya kware wajen satan mutane zaman shekaru 13 a gidan yari da horo mai tsanani, jami’an tsaro sun dade suna neman mai laifin ruwa a jallo.
The post Yan bindiga sunyi garkuwa da malamin Jami’a appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.