Ra’ayi:Ina ba Shugaba Buhari hakuri
Daga Edita: Wani tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai Abdulmumin Jibrin, ya bayyana yadda wasu ‘yan majalisar sukayi kari cikin kasafin kudi na shekara 2016
Wani mai sharhi a NAIJ.com Amb. Hussaini Coomassie,ya fadi ra’ayinsa game da abin kunyar nan na aringizon kasafin kudi. Marubucin yana mai bada hakuri ga shugaba Muhammadu Buhari
Ana iya cewa ban yi magana ba a lokacin, amma raina ya baci game da shugaba Muhammadu Buhari yayin da aka dauki lokaci wajen amincewa da kasafin kudi a lokacin. Bayan yaki sama kasafin hannu sai ma ya fice ya bar kasar kamar abin bai dameshi ba
Yanzu na amince Buhari kyautar Allah ne, kuma a cikin tarihin kasarmu shi yayi daidai kuma lokacin da ya dace
Bayan karanta jawabin tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Abdulmumin Jibrin, kan yadda akayi aringizo na sama da N200 biliyan cikin kasafin kudin, abin ya girgiza ni idan kayi tunanin cewa an dade ana yin irin haka sai kaji Kamar kayi haraswa
Ban yi mamaki ba tsohon shugaba Obasanjo ya kira ‘yan majalisar barayi shekaru da dama da suka wuce. Basu maida masa martani ba domin sun san ya sansu, kuma yana iya kara fallasa su. Baccin sa idon da Buhari da mukarrabansa suka yi da an Kara maimaita irin haka yayin da muke kallansu kamar wasu waliyyai bayan ko sun tatse mu sarai
Sanin haka yasa nike bada hakuri ga shugaba Muhammadu Buhari. Abin da yake bukata shi da mataimakinsa Prof. Osinbajo shine cikakken goyon bayan mu kan aikin da suke yi na maido da martabar kasarmu bayan satar fitar hankali da ” mutanen lema” suka yi ma kasar.
KU KARANTA :Jonathan ya kawo ziyara fadar Shugaban Kasa
The post Ra’ayi:Ina ba Shugaba Buhari hakuri appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.