Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Gwamnati ta raba awaki 720 ga mata, karfafa gwuiwa ne ko….?

0

-Gwamnatin jihar Katsina ta raba awaki 720 ga mata a shirinta na karfafa gwuiwa

-Awakin wadanda kudinsu ya kai N104 milyan an sawo su daga kasar Nijer

-Gwamnan jihar Aminu Masari yace N104 miliyan na cikin N2 biliyan da CBN ta bada bashi

Gwamnatin jihar Katsina ta sawo awaki 720 masu inganci wadanda kudinsu ya kai N104 miliyan domin rabawa ga mata cikin shirinta na karfafa gwuiwar mata.

Aminu Bello Masari, wani gwamnan jihar Katsina

Daily Trust ta ruwaito cewa mai baiwa gwamna shawara kan karfafa gwuiwa kan tattalin arziki Alhaji Abdulkadir Nasir ya ambaci haka yayin da yake kaddamar da shirin ranar Talata, 2, ga Agusta a Katsina

A cewar sa, kowace mace daga cikin mata 240 da aka zabo daga kananan hukumomi 34 da ke cikin jihar zata sami awaki  biyu da bunsuru daya. Ya kara da cewa an sawo awakin daga kasar Nijer, kuma suna da ingancin kiwo. Ya ci gaba da cewa

“An yi ma awakin Inshora na shekara daya, kuma lokitocin dabbobi zasu rika zagayawa domin duba lafiyar dabbobin”. Nasiru ya bukaci matan da kada su saida bisashen.

KU KARANTA : An kama wani mutumi yana kokarin cire kan abokinsa

Ya bayyana cewa gwamnati ta raba N30 miliyan ga mutane 1890 masu nakasa a jihar domin kafa kananan sana’u, haka kuma a kowace karamar hukuma an bada kudi ga mai nakasa guda domin kama shago, sayen janareta, kayan caji tare da jari na N20,000 domin saida katin waya. An raba kudi N340 miliyan ga masu kanan sana’u daga cikin N2.0 biliyan da babban bankin kasa ya bada rance ga jihar yayin da gwamnati ta dauki alkawarin biyan ruwan bashin na kashi 9 bisa dari.4

The post Gwamnati ta raba awaki 720 ga mata, karfafa gwuiwa ne ko….? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса