Allah ya yi: Kungiyar ‘Dream Team VI’ ta Najeriya ta isa Brazil
Allah ya yi: Kungiyar ‘Dream Team VI’ ta Najeriya ta isa Brazil.
Rahotanni masu zuwa mana nan NAIJ.com na tabbatar da cewa Kungiyar DREAM TEAM VI ta Najeriya ta isa Garin Manaus, na Kasar Brazil daf da za a fara buga wasan nasu. Najeriya dai ta isa Gasar Olympics din ne kimanin awanni bakwai kafin a buga wasan nasu, inda za su kara da Kasar Japan a wasan kwallon kafa na maza a Gasar na Olympics: Rio 2016. Najeriya tana Gurbi na Biyu (Group B) na wasan kwallon kafan maza a Gasar, inda za ta kara da Kasar Japan, Sweeden da kuma Columbia.
KU KARANTA: Yan Kungiyar DREAM TEAM ta Najeriya na nan carko-carko a Amerika.
Kungiyar ta DREAM TEAM da Samson Koci Siasia yake horaswa ta iso Manaus ne bayan da sun makale a Birnin Atlanta, na Kasar Amerika. An dai bayyana cewa Najeriya ba ta biya kudin Jirgi ba ne don haka aka hana su tashi zuwa Kasar Brazil inda ake gasar. Daga baya kuma suka samu aka warware wannan matsala, suka tashi zuwa Kasar Brazil da ake gasar. Yan Najeriya dai suna ta faman sukar wannan abin kunya, wasu har suna kira da a tsige Ministan wasanni na Kasar, Solomon Dalung. Najeriya dai ta saba zuwa duk irin wannan Gasa a makare, ko a shekarar 1996 inda Kasar ta lashe Gasar kwallon kafar maza, a makare Kungiyar kwallon kafar suka hallara, haka kuma suka ci gwal.
Ana dai sa ran Najeriya za tayi nasara a cikin sahun da ta ke; tare da Kasar Sweden, Columbia da kuma Kasar Japan a Gasar.
The post Allah ya yi: Kungiyar ‘Dream Team VI’ ta Najeriya ta isa Brazil appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.