Abin da ya sa Najeriya ba za ta mance da atlanta 96’ ba
ABIN DA YA SA NAJERIYA BA ZA TA TABA MANCEWA DA ATLANTA 96’ BA.
Najeriya na shirin fafatawa a Gasar Olymoics na wannan karo a Birnin Rio na Brazil. Duk da cewa an fuskanci matsaloli, daga rashin shiri zuwa na kudi da dai sauran su. Kasar ba za ta taba mancewa da Gasar Olympics na Atlanta 96 ba, a nan ne Kasar tayi zarra, inda ta ci gwal guda, zinarai biyu da kuma azurfa har uku a Gasar.
Ga dai dalilai 5 da suka sa Najeriya ba za ta mance da Atlanta 96 ba.
1. Kasar Najeriya ta ci Gwal a Kwallon Kafa
Kungiyar kwallon kafar maza ta zo na daya a Gasar, inda ta doke manyan duniya; irin su Brazil da Argentina a gasar. A wasan daf da na karshe, Brazil ta ci Najeriya 3-1 sai dai kafin a tashi labarin ya canza, Najeriya tayi waje da Brazil da ci 4-3. A wasan karshe, Emmanuel Amuneke ya ci ma Najeriya kwallon da aka tashi 3-2 da Argentina, Najeriya ta dauki kofi.
2. Chioma Ajunwa ta ci Gwal
Chioma Ajunwa ta ci ma Najeriya Gwal a Gasar Atlanta 96 wajen gudun ‘long jump’. Abin mamaki shine Yar wasa Chioma ba ta taba gwada wannan gudu a wata gasa ba, yin farko a Atlanta, sai ta tashi da makin mita 7.12. Har yau kuwa babu wanda ya kara ciyo ma Najeriya gwal tun ranar.
3. Mary Onyali ta zo ta uku
Mary Onyali ce ta zo ta uku wajen tseren mata na mita 200, cikin dakika 22.38. Ta zo bayan Yar Kasar Faransa da kuma Jamaica.
4. Tseren hadaka na Mita 400
Najeriya ta samu zinari wajen tseren mita 400 na mata (wanda mutane hudu ke shiga), Falilat Ogunkoya ta jagoranci Kasar. Sauran kuwa sune: Bisi Afolabi, Fatima Yusuf da Charity Opara. Najeriya ta zo ta biyu a wannan wasa cikin Minti 3:21:04, wata yar Amerika ta zo ta farko.
5. Ducan Dokiwari ya ci Azurfa a Dambe
Babban madambacin Najeriya Ducan Dokiwari ya zo na uku a wasa dambe a Atlanta 96. Tonga Wolfgramm ya buge sa da ci 6-7 rak a wasan kusa da karshe. Shi ya zo na uku a Gasar.
KU KARANTA: GASAR OLYMPICS: YAN KWALLON NAJERIYA SUN MAKALE
The post Abin da ya sa Najeriya ba za ta mance da atlanta 96’ ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.