Gasar Olympics: Darussa 5 daga wasan Najeriya da Japan
Gasar Olympics: Darussa 5 daga wasan Najeriya da Japan.
Kungiyar Dream Team VI ta Najeriya ta samu nasara kan Kasar Japan a wasan su na farko a Gasar Olumpics na wannan karo.
Ga abubuwa biya (5) da muka lura da su daga wasan na Najeriya:
- Dan wasa Mikel Obi ya buga wasa ne ba inda ya sa saba ba: An saka Mikel Obi a bayan dan wasa mai-cin kwallo Oghenekaro Etebo. Azubike ne kuma ya buga a ainihin gurbin dan wasa Mikel Obi. A kungiyar Chelsea, Mikel Obi yana tare ne, a wasan nan kuma an saka sa ya raba kwallaye.
- Najeriya ta fara shafa kwallo: Kwallon Kungiyar ya kara kyau kwarai da gaske, Kungiyar Dream team din ta fara raba kwallo da kyau a tsakiya, musamman daga wajen su Mikel, Azubike, Ezekiel, Amuzie da kuma Sadiq.
- Kwallo a Kafa: Babban abin da ya taimaki Samson Siasia shine yan wasan na sa suna da kwallo a kafar su. Sun san yadda ake shafa tamolen matuka. Sun kware wajen yanka, dai yan wasan na kuma bukatar karfin tuwo da kuma gudu wajen wasa.
KU KARNATA: YADDA NAJERIYA ZA TA KARYA LAGON JAPAN
- Baraka a baya: Akwai matsala a bayan Najeriya, domin kuwa tana rawa. Duk da cewa gaban Najeriyar na da kyau, to baya fa da kura. Hakan ya sa aka ci Najeriya kwallaye da dama, musamman idan aka ce maka an tsinke a guje. Yan wasan bayan namu; Ekong da Muhammad, basu gama fahimtar junan su ba. An ta samun kure daga bayan Najeriya.
- Shugabanci: Akwai tsarin shugabanci mai kyau a cikin fili (da ma wajen filin), za a yabi Kyaftin Mikel Obi da wannan. Kyaftin din na Kungiyar ne ya bar dan wasa Etebo ya dauki bugun finariti. Ko da aka cire sa daga karshe, sai ya mika ma Azubuike kambun kungiyar. Akwai tsari na shugabanci mai kyau a gaba daya Kungiyar, daga Koci Siasia har cikin yan wasa.
Duk da cewa dai Najeriya ba ta isa da wuri ba, ta samu nasara kan Kasar Japan da ci 5-4, ko da karshe dai, alamun gajiya ta nuna su.
The post Gasar Olympics: Darussa 5 daga wasan Najeriya da Japan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.