Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis
Ga bitar wasu fittatun labarai na ranar Alhamis 6 ga watan Agusta 2016
Shekau ya mayar da martani ga nadin sabon shugaba
‘Yan sa’oi kadan da kungiyar IS ta sanar da nadin Abu Mus’ab al Barnawi a matsayin sabon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau tsohon shugabanta, ya fitar da wani sakon muryarsa, a inda ya ke bayyana yadda ya ke ji game da nadin da kuma matsayinsa.
Kuma : Wata kungiyar yan bindigan Neja Delta sun fasa bututun mai
Kungiyar Tsageru ta Niger Delta Justice Defense Group NDJDG ta kai hari a kan wani bututun mai a Bera da ke karamar hukumar Gokana ta jihar Rivers a safiyar ranar Alhamis 4 ga wata.
Shugaban Boko Haram yayi barazanar kashe dukkan Kiristoci
Sabon shugaban Boko Haram wanda ya IS ta nada, ya yi hira da wata jaridar Al Naba a inda ya tattauna yakin da kungiyarsa ta Boko Haram ke yi da gwamnati.
Dallin da Goodluck Jonathan ke ziyartar Shugaba Buhari da dare
Shugaba Buhari ya gana da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a fadar Aso Rock da ke Abuja a ranar Laraba 3 ga watan Agusta, ganawar ta su ta kimanin minti 20 ana rade-radin ya karkata ne ga rikicin yankin Niger Delta.
Sarki Sanusi ya jaddada cewa tallafin kudin mai cuta ne
Gasar Olympics: Yan kwallon Najeriya suna nan cirko-cirko a Amerika
The post Waiwaye: wasu fittatun labarai na ranar Alhamis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.