Nigeria ta lallasa Japan a wasanta na farko a Brazil
-Najeria ta doke Japan da ci 5 da 4 karawar su a gasar Olympics
-Yanzu ita cwe kan gaba a rukunin B
-Etebo ne ya zura kwallaye 4 a mintuna 5 da fara wasa
-Sadiq Umar ne ya fara zura kwallo
‘Yan wasan Najeriya na zura kwallo a ragar ‘yan Japan jim kadan da fara wasa
Dan wasa CD Feirense star Oghenekaro Etebo ya fidda da Nigeria kunya, ya kuma dauki hankalin ‘yan kallo a karawar kasar da Japan a gasar Olympics da ake gudanarwa a Rio ta kasara Brazil. ‘Yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 23sun lallasa ‘yan Japan ne da ci 5-4 a karawar da suka yi a filin wasa na Manaus da ke Brazil. Etebo ne ya zura kwallaye hudu a ragar Japan bayan da Sadiq Umar ya share fage da cin fari.
KU KARANTA: Dan wasan Super Eagles, Mikel Obi yayi sabon suna
Wannan shi ne wasan kasashen biyu na farko a gasar ta kuma wasan kwallon kafa na farko a gasar guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics da ake gudanarwa a Rio ta kasar Brazil ‘Yan wasan Najeriya sun yi bazata ganin yadda suka sauka a Brazail din ba a cikin shiri ba, bayan da suka makale a Atlanta ta Amurka na tsawon lokaci, daga baya suka samu isowa sa’o’i kimanin sa’oi biyar kafai a soma wasa, ana kuma sa rai ‘yan wasan za su yi rawar gani, kasancewar wasu kwararru kuma fittatun ‘yan wasan irin su Mikel Obi a cikin masu bugawa kasar
Sauran jerin ‘yan wasa: 18. Emmauel Daniel, 2. Seth Muenfuh, 4. Abdullahi Shehu, 6. Williams Troost-Ekong, 8. Oghenekaro Etebo, 9. Imoh Ezekiel, 10. John Obi Mikel (Kyaftin), 13. Sadiq Umar, 14. Azubuike Okechukwu, 16. Stanley Amuzie, 17. Usman Muhammed. Subs: 3. Kingsley Madu, 5. Saturday Erimuya, 7. Aminu Umar, 11. Junior Ajayi, 12. Popoola Saliu, 15. Ndifreke Effiong.
Mai horas da ‘yan wasa: Samson Siasia
The post Nigeria ta lallasa Japan a wasanta na farko a Brazil appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.