Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Ya kamata a daure Jose Mourinho-Inji Jami’in FIFA

0

– Wani Jami’in Kungiyar FIFA na son ganin an daure Kocin Man Utd Jose Mourinho.

– Jami’in Dejan Stefanovic na ganin abin da kocin yake yi ma dan wasa Schweinsteiger, sam bai dace ba.

– Tsohon dan wasan Stefanovic, yace kyaun ta garkame Jose Mourinho na shekara uku.

 

 

 

 

 

 

Wani babban lauya, kuma Jami’in Kungiyar FIFA ta duniya Dejan Stefanovic yace Kocin Man Utd Jose Mourinho ba karamin maketaci bane, ganin abin da yake faruwa da dan wasa na Bastian Schweinsteiger na Kungiyar. Jami’in yana ganin cewa ya kamata a kama Mourinho, a daure a gidan yari saboda ajiye dan wasa Schweinsteiger Bastian da yayi a cikin sahun ‘yan baya tun da ya zama Kocin Kungiyar ta Man Utd. ‘Wannan ba karamar keta bace…’ Stefenovic yake fada ma Jaridar Mirrror UK, ta Birtaniya. ‘Da ace a Kasar mu ne, ta Slovenia da mun sa an kama sa (Mourinho Jose), a hukanta sa da horo mafi tsauri, shekaru uku a gidan yari. Bai dace ayi ma Bastian (Schweinsteiger) haka ba, sai mun je Kotu…’ Inji wannan Jami’i. Stefanovich yana ganin ai kawai dan wasa Schweinsteiger ya kai karar Kocin nasa wajen Kungiyar PFA, domin a hukunta sa.

KU KARANTA: BA NI BARIN CHELSEA INJI MIKEL OBI

Tsohon dan wasan na son ganin an canza dokokin wasan. Dole dan wasan da ke bugawa Kungiya yayi wasa cikin sauran yan uwan sa tare kuma da Kocin Kungiyar, ba kawai a jefa sa cikin yan yara ba. Stefanovic na son Hukumar FIFA ta canza dokar. Kungiyar man Utd din dai bat ace komai game da wannan magana da Jami’in Kungiyar FIFA ta duniya yayi. Dan wasa Bastian Schweinsteiger mai shekara 32, bai buga wasan da aka buga a Filin Old Trafford ba tsakanin Kungiyar Everton da Man Utd, duk da kuwa Jose Mourinho yayi amfani da yan wasa fiye da 20 a wasan.

 

The post Ya kamata a daure Jose Mourinho-Inji Jami’in FIFA appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса