Gasar Olympics: Kasar Afrika-ta-Kudu ta rike Brazil
– Kasar Afrika-ta-kudu ta rike Kasar Brazil a gida, a wasan farko na Olympics.
– An tashi babu ci a Karshen wasan.
– Haka nan ma dayan wasan da aka buga, babu wanda yayi nasara.
Kasar Afrika-ta-Kudu ta rike Kasar Brazil duk da jan kati a wasan farko na Gasar Olympics wanda ake bugawa a Kasar Brazil din. An dai tashi wasan ne babu wanda yayi nasara, 0-0. Bakin na Nahiyar Afrika sun rike Brazil ne har aka tashi ba ci a wasan su na Duron farko na Gasar kwallon kafar wannan karo a filin wasa na Mane Garrincha da ke Kasar ta Brazil.
KU KARANTA: PEP GUARDIOLA YA SAYO WANI DAN WASA DAGA BRAZIL
Kasar Afrika-ta-kudu ta fara wasan da kyau, sai dai ba ta samu bude zaren na Kasar Brazil ba duk da hare-haren da tayi ta kai wa. Sai ga shi daga reshe ya juya da mujiya, Kasar Brazil ta ritsa Afrika-ta-kudu gaba, Dan wasa mai tsaron gida Itumeleng Khune na Kasar Afrika-ta-kudu ya kabe wasu kwallaye daga wajen dan wasa Neymar Jr. kafin a tafi hutu rabin lokaci, ko da aka tashi wasan, Golan na Kasar Afrika-ta-kudu ne gwarzon yinin. Dolly, Gift Motupa da Mezi Masuku sun yi kokari wajen cin kwallo, sai dai abin ya ci tura, Dan wasa Dolly ya barnatar da wani kwallo da aka dago masa daga bugun ‘corner’, daga shi sai raga, amma ya jefa ta wani wuri dabam. A minti na 59 ne wasa fa ta canza, alkalin wasa ya ba Mvala Mothobi na Afrika-ta-kudu katin gargadi karo na biyu, wannan yana nufin an sallame sa kenan daga wasa, wannan ya zo ne bayan da dan wasan ya gwabje Neymar na Brazil. Haka Kasar ta sa ta buga wasa babu mutum daya har na tsawon minti talatin.
Ba dan gola Khune ba kuwa da an lallasa Kasar, an dai tashi wasan 0-0, kamar yadda aka kare tsakanin Kasar Iraki da Denmark.
The post Gasar Olympics: Kasar Afrika-ta-Kudu ta rike Brazil appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.