Aisha Buhari ta halarci taron US Institute of Peace
Bayan zargin cewa ta sauka kasar Amurka tare da jakar da darajar sa ta kai kimanin naira milliyan 34, an hangi Aisha Buhari, matar shugaban kasar Najeriya, tana halartan wani taro a kasar.
Hotunan da aka samu daga Sahara Reporters ya nuna cewa matar Buhari na cikin jin dadi da kwanciyar hankali da halin farin ciki a lokacin da take halartan wani taro a United State Institute of Peace hade da kungiyar watsa labaran muryar Amurka
Alamun ta ya nuna cewa zata dauki kimanin kwananki goma(10) a ziyarar da ta kai kasar shugaban kasa Barrack Obama, kuma matar shugaban kasar Najeriya ta nuna alama juna da rahoton dake cewa tayi tafiya tare da irin wannan jaka mai tsada.
Cikin sauran taron da ake sa ran zata halarta sun hada da taron dangantaka a jami’ar Gorge Mason dake Fairfax, Virginia da kuma taron murnan zagayowar ranar kungiyar Zumunta karo na 25 a USA Inc.
Aisha Buhari a lokacin taro a United States Institute of Peace a ranar Alhamis 4 ga watan Augusta na shekara 2016. Hoto:Sahara Reporters.
Aisha Buhari tare da sauran mutane a gurin taron a ranar Alhamis 4 ga watan Augusta. Hoto:Sahara Reporters.
KU KARANTA KUMA: Mambobin APC 700 sun koma PDP
A lokacin da ta isa kasar Amurka, an rahoto cewa matar shugaban kasa ta samu tarba daga jakadiyar Najeriya a kasar Amurka, wasu matan gwamnonin Najeriya, kungiyar Zumunta babin Amurka, da yan Najeriya mazauna kasar.
Haka kuma sukar da Ayo Fayose, gwamnan jihar Ekiti yayi, na zargin cewa matar shugaban kasa na da hannu cikin abun kunyan Halliburton, kuma cewa bata isa ta kai ziyara kasar Amurka ba don tsoron kar a kama ta, yasa ana ta izgilanci gad an siyasar kuma ana ta nuna jin dadi ga matar shugaban kasa.
The post Aisha Buhari ta halarci taron US Institute of Peace appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.