Sakwanni 10 daga fina-finan Yarbawa ga mai kallo
Sola Bodunrin ya gano wasu sakwanni 10 da ke kunshe a cikin fina-finan da ake yi da Yarbanci wadanda ba lallai ne su zama gaskiya ba, amma dai kowanne tsuntsu kukan gidansu ya ke yi
Basaraken Yarbawa Ooni na Ife tare da matarsa Olori
1. Kishiyar uwa ba uwa, ba uwa ba ce: Lallai ka guji kishiyar uwa domin za ta iya canza makomarka ta alheri da na dan ta. Watau ta na iya canza kaddara.
2. Shakuwar miji da ‘yar uwar mata, hadari ne: Idan ki ka fahimci mijinki ya shaku da ‘yar uwar ki, ko da ciki daya ku ka fito, to nemanta ya ke a waje!
3. Miji ba shi da hutu da dare: Matar Bayarbe a shirn fim ba ta da lokacin da za ta tattauna matsalar gida da mijinta sai da tsakar dare.
4.Boka da malam da Fasto sun ne kat! Duk wata matsala ba a danganta ta ga Allah don neman waraka.
KU KARANTA: An gargadi wani dan fim kan taba Buhari
5. Mai aiki ko matar gida? Ba abin mamaki ka ga mai aikin gida ta tsoma baki a cikin maganar masu gida, ta kuma yi kane-kane. Anya kuwa?
6. Komai ka yi da jaki…:‘Yan aikatau kidahumai ne: duk ‘yar aikin gida da fina-finansu tabbata kidahuma ce ko kuma dakikiya, haka ma mazansu.
7. Tsafi ne mafita: da zaran mutum ya shiga wata matsala ta rayuwa, shawara ta farko ita ce, ya yi fashi da makami ko yankan kai
8. Mata su ne ummulhabaisin rashin haihuwa kurunkus!
9. Bayan mutum ya amsa laifinsa na yiwa wani asiri, sai soma hauka daga nan sai mutuwar wulakanci
10. Maganin gargjiya ya fi na bature: Shawarar kowanne likita shi ne ka koma ka yi na gargajiya
The post Sakwanni 10 daga fina-finan Yarbawa ga mai kallo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.