Yan fashi sun kashe wani mai babur
A ranar Alhamis, 4 ga watan agusta yan fashi sun kai hari ga wani mai babur mai kafa uku wanda aka fi sani da keke nspeo a Jihar Kano.
An bada rahoton cewa sun yi kokarin kwace masa babur din sa shi kuma ya kiya sai suka daba mai sara a bayan wuyan suka kaishi hat lahira. Wani abu shine kuma barayin basu samu daman tafiya da babur din ba. An birne mutumin a bisa koyarwan addinin musulunci a garinsu.
KU KARANTA : Likita ya manta da tawul a cikin wata mata.
A musulunce ana daukan irin wannan rasuwa mutuwan shahada, saboda hadisin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce duk wanda aka kashe akan dukiyarsa ko kare iyalinsa yayi mutuwan shahada.
The post Yan fashi sun kashe wani mai babur appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
