An biya fansan dan majalisan nan N10 million
–An yi garkuwa da hon. Sani Bello , wani dan majalisan wakilai ta kasa tare da ma’aikacin sa a gonarsa da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.
–Duk da cewan yan sanda sun ce basuda masaniya akan fansan, shugaban jam’iyyar APC ta jihar katsina yace Bello ya samu yanci bayan an biya kudi N10 million.
Sani Bello bayan am biya fansan miliya 10
Hon. Sani Bello, wani dan majalisan wakilan tarayya mai wakiltar mazaban Mashi/,Dutsi a jihar Katsina ya samu yanci kwanaki biyu bayan an yi garkuwa da shi a gonan shi da ke birnin gwarin jihar Kaduna. An saki Sani Bello ne bayan an biya fansan kudi N10million .
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa an biya kudin ne domin a sake shi da ma’aikacin sa da aka yi garkuwa da su tare. Anyi garkuwa da su ne a kauyen gobirawa dake garin Birnin Gwari, Kaduna. Tabbatar da sakin sa, shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Shittu Shittu ya laburts cewan an sake shi bayan sun biya wasu kudade.
Yace: “Masu garkuwa da mutanen sun ce direban dan majalisan ya kai kudin wani wurin kuma bayan mintuna 15 zuwa 20 suka sake shi.
KU KARANTA : Yan bindiga sunyi garkuwa da malamin Jami’a
Information Nigeria ta bada rahoton cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi fansan ne ba tare da ilimin yan sanda ba. Yin garkuwa da mutane ya zama kasuwanci da ya bunkasa yanzu a wannan kasa ta mu sakamakon rashin aikin yi ga samari matasa da kuma samun kananan makamai.
Yayinda wasu yan Najeriya ke neman a samu jami’an yan sanda na jiha, majalisan dokokin jihar Legas ta yi dokan dubin makwabci.Wannan dokan Har yanzu da gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode bau sa hannu ba. Wani tsohon dan majalisan Jihar, Mufutau Egberongbe , yace Idan gwamnan ya sa hannu, zai rage rashin zaman lafiya a jihar.
The post An biya fansan dan majalisan nan N10 million appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
