Wasu yan Najeriya suna sukan rage farashi ga mahajjata
Wasu yan Najeriya na sujan umarnin da babban bankin Najeriya CBN na cewan a sayar ma mahajjata masu zuwa aikin hajjin bana dalar Amurka a farashin N197/$.
Game da Jaridar Vanguard, babban bankin ta bada umurni ga bankunan Najeriya da wasu yan kasuwan canji da sayar ma masu niyar zuwa hajji dala a farashi mai sauki.
Islam
CBN ta bayyana hakan ne a ranan alhamis, 4 ga watan agusta ,tace : “Duk wani mahajjaci nada hurumin sayan dala akalla $750.00 kuma akasarin $1000,00 a matsayin guzuri. Saboda haka, gwamnatin tarayya ta amince da a sayar ma masu niyyar zuwa hajji dala a farashin N197/1$ .
“Babu kwamishon da wata bankin najeriya zata karba a hannun mahajjata . Babban bankin tarayya zata sayar da tallafin ga wasu bankuna ta musamman a jihohin Legas da Abuja ,kuma za’a biya kudin tallafin muddin an biya kudin ga bankunan baki daya.”
KU KARANTA : Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro
Amma yan najeriya musamman mabiya addinin kirista sun fara sukan haka. Sun ce duk da halin durkushewan tattalin arzikin kasa da a keyi gwamnati na irin wannan.
The post Wasu yan Najeriya suna sukan rage farashi ga mahajjata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.