Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Ba zan daina fashi ba-inji dan fashin da aka kama

0

Wani dan fashi dan shekaru 24 mai suna Richard Akinwale ya bayyana cewa ba zai daina sata ba, tunda bai ga abin kyama a cikin harkar ba.

Akinwale

Akinwale yayi wa yansanda wannan bayani ne bayan an kama shi a ranar laraba 3 ga watan agusta da laifin satar motar mai gidansaa ranar 8 ga watan yulio. Duk da cewa ubangidan nasa yayi belinsa, sai ya sake komawa ya saci motar karo na biyu, wanda yayi sanadiyyar yansanda suka sake kama shi.

Yan sanda sun gabatar da Akinwale ne a caji ofis na Ogbongo, Akinwale ya taba zama dalibin wata jami’a a kasar kwatano, amma daga baya aka kore shi. Rahotanni sun nuna cewa Akinwale ya samu shiga gadin maigidan nasa ne ta silin, inda ya kwashe kayan dakin tare das ace motar mutumin. Yace ya saci motar ne kawai don ya bata ma mutumin rai, duk da cewa shi ya dauki nauyin karatunsa.

A yayin da Adelabu ke tsokaci kan halayyar Akinwale, yace “ina tsoron kada ya bata min yaya ne, saboda su ma sun fara girma. A lokacin da ya saci motar a karo na farko, nayi kararsa a ofishin yan sanda na Ogbongo dake yankin Ajah. Yansanda sun kama shi a washegari, inda suka daure shin a tsawon wasu kwanaki. Daga bisani na roki DPO ya sake shi.

Nayi tunanin zai canja halinsa, sai dai abin mamaki, bayan kwana biyu sai ya koma ya sake satar motar. A wannan lokaci sai nayi kararsa ga yansanda na musamman masu yaki da yan fashi, inda suka kai samame a unguwar agege, inda anan aka kama shi.”

Hmmmmm…wai shi yafi son sai an kashe shi ne zai bar sata?

The post Ba zan daina fashi ba-inji dan fashin da aka kama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса