An ci gaba da tsare mai Kare da sunan Buhari
-An gurfanar da mutumin da ya sa wa karensa Buhari a gaban kotu
-Kotu ta bayar da belinsa amma ya kasa cika ka’idoji
-Makwabcin maikaren ne ya kai kararsa wurin ‘yan sanda
Mai sana’ar Tireda a jihar Ogun Joe ya sake kwashe kwanaki 3 a gidan yari a jihar Ogun bayan da iyalinsa suka gaza cika ka’idojin belin da kotu ta shimfida masa, a cewar jaridar Vanguard.
Kotun Majistare da ke zamanta a jihar Ogun ce ta bayar da belin Joe, bayan ta saurari karar da aka kai shi a bisa laifin sa wa Karen sa suna ‘Buhari,’ da kuma nuna halayyar da ka iya haddasa fitina a jihar, kotun ta bayar belinsa a kan Naira dubu 50,000 da kuma gabatar da wadanda za su tsaya masa su biyu suma a Naira 50,000 kowannensu.
‘Yan uwansa sun fadawa manema labarai cewa, sun gaza samun kudin in ban da Naira 20,00 da suka tattara, har yanzu ba su samu cikon ba, a cewa mata majiya, iyalan sun roki hukumomin jihar da su taimaka su karbi abin da ya ke hannunsu, su kuma saki dan tiredan.
KU KARANTA: Rana za ta yi khusufi a Nigeria a farkon watan gobe
Sai dai ba a sani ba ko hukumomin sun ji rokon nasu, sai dai wata majiya ta ce, ta ga jami’ai na daukar bayanan mutane biyun da za su karbe shi beli da misalin karfe 3:30 na yamma a ranar Laraba 24 ga watan Agusta.
Wani mai suna Halilu Umar Sokoto makwabcin mai Karen ne ya kai kararsa wajen ‘yan sanda, a bisa zargin cewa sunan mahaifinsa Alhaji Buhari ya sa wa Karen, yayin da a gaban kotu mai kare Joe ya ce, ya sa wa Karen sunan ne domin kaunarsa da shugaban Buhari.
The post An ci gaba da tsare mai Kare da sunan Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.