Rahotanni sun bayyana cewa jerin gwanon ayarin motocin rakiyar gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa sun hallaka wani dattijo ta hanyar bankade shi a unguwar Umutu dake karamar hukumar Ukwuani, yankin kudu maso kudun jihar.
Kamar yadda rahotan Sahara Reprters ya nuna, lamarin ya afku ne da yammacin ranar juma’a 19 ga watan agusta yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta dawowa daga taron jihohin Neja Delta wanda ya shirya tare da Edwin Clark.
Rahoton ya kara da cewa wasu ma’aikatan jarida sun samu raunuka, haka nan ma direban motar mai suna Isaac. Motar yan jaridun gwamnatin jihar ne ta bankade dattijon lokacin da yake cikin motar akori-kura.
Nan da nan aka garzaya da dattijon zuwa asibitin Abraka inda aka turasu asibitin Asaba inda yace ga garinku nan, sakamakon karancin jinni da yawan raunuka a jikinsa. Saura kiris lamarin ya janyo hayaniya, wanda hakan ya sanya gwamnan saukowa daga motarsa yaje ya baiwa samarin unguwar hakuri.
“Isaac ne tuka motar da ta kashe dattijon, inda daga nan ya rasu. Yan jaridu da dama sun ji raunuka, wanda saura kiris da sun mutu, daga bisani an garzaya dasu asibitin gidan gwamnati. “saura kiris samarin unguwar su kone motocin gwamnan da na sauran manyan jami’an gwamnati.
“sai da gwamna Okowa ya sauko daga motarsa ya basu hakuri. Har zuwa yanzu direban motar na daure a hannun yansanda”. Inji majiyar mu. Gwamna Okowa ya shirya tura ayarin wakilansa don jajenta ma iyalan dattijon, da kuma shirin biyan su diyya.
Чемпионат по военно-спортивному многоборью среди росгвардейцев завершился в Грозном
«Краснодар» и московское «Динамо» проведут сегодня первые матчи в Кубке России
Легкоатлеты из Мордовии показали лучшие результаты мирового сезона на международных соревнованиях в Москве
В День парашютиста героем рубрики «Знай наших» стал сотрудник вневедомственной охраны столичного главка Росгвардии младший лейтенант полиции Александр С.
Два человека пострадали при обвале скально-грунтовой породы в Кисловодске
Августовский урожай. Сезонные ягоды и фрукты, которые стоит купить сейчас
"КИБЕР ПУШКИН": МНОГО НАТО НЕ НАДО ХОРОШИМ ДРУЗЬЯМ, И ВООБЩЕ: НАТО ВСЕМ ОЧЕНЬ, ОЧЕНЬ НЕ НАДО! СЕНСАЦИЯ! Россия, США, Европа могут улучшить отношения и здоровье общества!
Мэр Кисловодска Моисеев: под завалами грунта в санатории может быть человек