Kwanan nan makwabta wata matar kasar Rasha da ba’a ambaci sunanta ba suka kamata da gawan mijinta da ya mutu.
Bisa ga rahoto daga Meduza, tsohuwar mai shekaru 76 bazata iya jure rashin mijinta abun sonta mai shekaru 87, hakan ne yasa bata fada ma jama’a muturwan mijin nata ba. Maimakon hakan ma, sai ta dauki tsawon watanni hudu tana kokarin dawo dashi duniya da taimakon wani ruwan mai tsarki da kuma addu’a.
Makwabta sunji alamun wani bakon abu yana aukuwa a ranar 12 ga watan Augusta, lokacin da ta zubar da ruwa a kasa ba tare da saninta ba, sai wani makwabcin ta ya shiga gidanta domin ya kashe ruwan. A nan ne ya ka gawan mijin nata a kwance magashiyan a falon kidan sai ya kuma sanar da yan sanda a take. Masana akan cututtuka sun kayyade cewan mutumin ya kai kimannin watanni hudu zuwa shidda da mutuwa, amma kuma ba’a samu ko wani rauni a gawansa ba kuma an yanke cewar mutuwar Allah ce.
A lokacin da ake bincike, makwabta sun bayyana cewa sunji wani bakon wari na fita daga dakin na dan wani lokaci, amma basu yi tunanin komai a kai ba. Haka kuma mutumin yaji wani mugun rauni a kafar a sa a shekara ta 2015 don haka yake kwance tun lokacin, don haka babu wanda yasan halin da yake ciki sai matar sa. Domin ta tabbatar da cewa babu wanda ya bata mata shirinta na son dawo da wanda ya mutun, matar tana fada ma duk wanda ya tambayeta lafiyar mijinta cewa yana nan lafiya amma baya son ganin baki. Har yayanta bata fadama gaskiya lamarin ba kuma ta hanasu ziyara, saboda su duka biyun suna lafiya.
A lokacin bincike yan sanda sun gano cewa tsohuwar wacce tayi aiki a matsayin likita lokacin kuruciya, kuma tana son ta kwaikwayi aikin Leonid Konovalov, wani dan kasar Rasha wanda yayi shiri a inda yake Magana da matattu.
“Lokacin da fara zantawa da matar, ta bayyana cewa idan ta zuba ruwan a kan mijinta, ta hanyar ne zata iya dawo da mijinta duniya,cewar mai bincike Milena Fratsuzova.
Сотрудница подразделения столичного главка Росгвардии завоевала «золото» на чемпионате войск по легкоатлетическому кроссу
Легкоатлеты из Мордовии показали лучшие результаты мирового сезона на международных соревнованиях в Москве
«Краснодар» и московское «Динамо» проведут сегодня первые матчи в Кубке России
В День парашютиста героем рубрики «Знай наших» стал сотрудник вневедомственной охраны столичного главка Росгвардии младший лейтенант полиции Александр С.