Yan bindiga sun kuma kai hari a Legas; karanta abunda sukayi wa mutane uku a unguwa
– Da alama yan bindiga sun sauya salon ayyukansu a jihar Lagas kamar yadda aka sace masu gida uku
– Yan sanda sun tabbatar da sace mutanen kuma sunyi alkawarin ceto wadanda abun ya cika da su
– Ana zargin yan bindigan sun badda kama a matsayin sojoji suka kuma sace mutane uku
An bar yan Unguwar New Heaven cikin tsoro bayan yan fashi da makami da suka sauya kamanni kamar sojoji sun sace wasu mutane uku.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun mamaye unguwar wanda ke Igbelaju, a yankin Iba dake jihar Lagas a ranar Asabar da ranar Litinin.
A lokacin harin na farko a ranar Asabar, yan bindigan da ake zargi sun sace wata Mrs. Nwoche daga gidanta kuma har yanzu ba’a sake ta ba.
Kwanaki biyu da yin haka, sun kuma kai hari inda suka kuma sace mutun biyu wadanda suke tukin fita daga unguwar suka Cuma umarce su da su fito dauke da bindiga.
KU KARANTA KUMA: Fani-Kayode ya goyi bayan a raba Najeriya
Ebuka wanda ya kasance mai tukin babur a unguwar yace, yan bindigan sun zo a matsayin sojoji ne a safiyar washegarin ranar da suka sace Mrs. Nwoche.
Hanyar da yan bindiga suka tsere bayan sun sace mutane uku
“Bana nan lokacin da al’amarin ranar Asabar ta faru saboda ya faru ne da misalign karfe tara (9) na safe kuma mutane sun dai ji tashin karar bindiga ne kuma suka gudu cikin gidajen su. Yan bindigan suka tafi tare da wata mata wacce ke zaune a babban gidanta. Bata dawo ba har yanzu.
“A ranar Litinin, yan ta’addan sun zo ne da safe. zaka zata sojoji ne wanda suka zo duba unguwar. Na gansu sanye da kayan sojoji tsaye kusa da wani gadan katako kuma rike da bindiga.
KU KARANTA KUMA: Ku Kwaikwayi dokar kiwon dabbobi- MASSOB sun fada ma gwamnoni
“Na zo wuce wa dauke da pasinja, amma na gansu dauke da bindiga, wasu yan sa’aoi kadan si suka tsayar da wasu mutane biyu dake tuki a hanyar fita daga unguwar. Mutanen na cikin motoci daban-daban ne amma suna bin juna.
“Sun umurce su da su fito su biyo su. Ta haka ne suka dauke mutanen guda biyu. Har yanzu bamu ga ko daya daga cikinsu ba. Kowa najin tsoro.”
Dolapo Badmos wanda ke Magana da yawun yan sandan jihar Lagas ya tabbatar da sace mutanen ya kuma ce an rigada an fara kokarin ceto su.
Yan bindiga na addabar wasu yankuna dake jihar Lagas a makonnin da suka wuce musamman a yankunan dake kusa da ruwa.
The post Yan bindiga sun kuma kai hari a Legas; karanta abunda sukayi wa mutane uku a unguwa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.