Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Сентябрь
2016

Modu Sheriff yayi ganawar sirri da Obasanjo

0

Ali Modu Sheriff dake ikirarin shugabancin jam’iyar PDP yayi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Sheriff da Obasanjo

Ganawar ta gudana ne a gidan Obasanjo dake kan tsauni a birnin Abekuta na jihar Ogun.

Sheriff ya hallara gidan Obasanjo ne cikin wata motar alfarma kirar marsandi mai lamba AAA 673 BL da misalin kafe 11:40 na safe cikin a yarin motoci guda hudu yan rakiya.rahotanni sun nuna motar da sheriff ke ciki ne kadai aka bari ta shiga harabar gidan Obasanjo, inda sauran hudun suka jira shi a waje.

Sheriff ya zarce har cikin uwar dakan Obasanjo inda suka gana a asirce, ganawar da ta dau kusan awa daya.

Ana has ashen ziyaran da sheriff ya kai ma Obasanjo baya rasa nasaba da rigimar shugabanci daya dabaibaye jam’iyyar tasu ta PDP, rigimar tayi sanadiyyar darewar jam’iyar gida biyu, inda Ali Modu Sheriff ke shugabantar bangare guda, Sanata Ahmad Makarfi na jagorantar bangare guda.

A ranar 21 ga watan Mayu ne dai masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka tsige Ali Modu Sheriff daga shugabancin jam’iyyar, sai dai Sheriff din yaki amincewa da tsigewar, kuma ya cigaba da musanta batun. Yanzu haka jam’iyyar na fuskantar shari’u daban daban a gaban kotuna iri iri.

Sanata mai wakiltan al’ummar Ogun ta tsakiya Buruju Kashamu ya shawarci shuwagabannin PDP su cire ran za’a iya warware matsalolin jam’iyyar tasu daga nan har zuwa 2019.

The post Modu Sheriff yayi ganawar sirri da Obasanjo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса