Jami’in watsa shirye-shirye Olalomi ya kwanta dama
– Wani Jami’in watsa shirye- shirye mai suna Surajudeen Taiwo salami wanda akafi sani da Olalomi Ejire ya kwanta dama
– Mai watsa shirin ya rasu ne a ranar juma’a, 2 ga watan satumba a asibitin jami’ar Legas, Idi- Araba, bayan yayi gajeruwar jinya
– Olalomi Ejire ya na watsa shiri nd a gidan rediyon Legas da Faaji Fm har karshen rayuwarsa
Olalomi Ejire
Wannan sanannen Jami’in watsa shirye- shirye mai suna Surajudeen Taiwo salami wanda akafi sani da Olalomi Ejire ya rasu.
Olalomi Ejire ya rasu ne a ranar juma’a, 2 ga watan satumba a asibitin jami’ar legas ,idu Araba, bayan yayi gajeruwar jinya.
KU KARANTA: An kashe abokin Gwamna Mimiko
Game da cewar gwamnan kungiyar masu watsa shiri a najeriya watauFreelance and Independent Broadcasters’ Association of Nigeria (FIBAN) ,shiyar Jihar Legas, Yomi Mate Ifankalleluyah, yace an birne shi game da koyarwan addinin musulunci.
Olalomi ,mai watsa shiri ne kuma mai jagorantan shirin Eko lawa a rediyon jihar legas da kuma Ogbon Kayeso a Faaji FM. Dan kungiyan FIBAN ne kafin rasuwar sa. Marigayin ya rasu a shekara 54 ,kuma dan asaln Agaka, Ede, jihar Osun .
The post Jami’in watsa shirye-shirye Olalomi ya kwanta dama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
