Tashin hankali yayinda shugaban Arewa yayi kira ga zanga-zanga kan Buhari
– Shugaban Arewa, Balarabe Musa yace Yan Najeriya su kare kansu saboda gwamnatin Buhari tana wasa da rayukan su
– Balarabe yace yunwar dake addabar kasar ta isa ta haddasa tawaye ya kuma amince yan Najeriya suyi zanga-zanga kan wahalar saboda rayukansu na cikin hatsari
Balarabe Musa yace yan Najeriya suyi zanga-zanga kan buhari
Shugaban Arewa kuma shugaban jam’iyyar Conference of Nigeria Political Parties (CNPP), Balarabe Musa ya fada wa Yan Najeriya da suyi zanga- zanga ga gwamnatin Shugaban kasa Buhari.
KU KARANTA KUMA: Sakatariyar ogun ta mutu sa’o’i 24 bayan an rantsar da ita
Jaridar Daily Post ta nakalto Balarabe kamar yadda ya gaya wa jaridar The Sun a wata hira cewa Yunwa na da karfin da zai jawo zanga-zanga kuma tunda gwamnatin yanzu ta gaza ga tabbatar da tsaro da kuma abinci, toh yan Najeriya na da daman kare mukatunsu ta yin zanga-zanga.
Duk da haka, ya yarda cewa wannan zai iya samun koyarwar sakamako ga gwamnatin Buhari.
KU KARANTA KUMA: Ku zo mu hada hannu tare mu yaki ciwon yunwa- Aisha Buhari
A halin yanzu, Sanata Dino Melye, wanda ke wakiltan jihar Kogi maso yamma a Majalisar dattawa, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matakai kan Farfadowar tattalin arziki, ciki harda dakatar da Ministan kudi, Kemi Adeosun, Ministan kasafin kudin kasa, Sanata Udo Udoma da kuma Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele cikin gaggawa.
Melaye a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba, yace ya zama dole shugaban kasa ya girgiza yan majalisar sa da wasu mambobin majalisar da aka zarga da cewa basu da abunda ya dace gurin gudanar da ma’aikatar su da hukumominsu.
The post Tashin hankali yayinda shugaban Arewa yayi kira ga zanga-zanga kan Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.