Wasu Sojoji na sayar da makamai ga ‘yan Boko Haram
– Bincike ya nuna cewa wasu Bata-garin Sojojin suna sayar da makamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram
– Ana binciken wasu manyan Sojojin Kasar da wannan aika-aika na satar makamai, suna kuma aikawa da su ga ‘yan ta’adda
– Manjo-Janar Lucky Irabor ya bada tabbacin wannan maganar, ya kuma bayyana hakan da cin amanar al’umma
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Bincike sun nuna cewa wasu daga cikin manyan sojojin Najeriya suna aikawa da Makaman Kasar zuwa ga ‘yan Ta’addan Boko Haram. An buga wannan sabon bincike ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba nan a Kafar Associated Press. An bayyance cewa ana biciken wasu manyan Sojojin Kasar da aikata wannan mugun laifi.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun daura Damara da masu satar mutane
Manjo-Janar Lucky Irabor ya tabbatar da cewa wasu manyan Sojojin Kasar na sace makamai, suma kuma sayarwa zuwa ga ‘yan ta’adda. Manjo-Janar Lucky Irabor yayi wannan jawabi ne a wani taro a ranar Alhamis din da ta gabata. Manjo-Janar Irabor ya bayyana wannan abu da cin amanar al’ummar kasa.
Wani Soja da ke filin daga ya bayyanawa Kafar ‘Associated Press’ a sake cewa, wasu daga cikin wadanda ake bincike a Gidan Soji da wannan laifi sun hada har da kwamandan barikin su. Ana gudanar da wannan bincike ne a boye. Sojin na binciken yadda aka yi wasu bindigogi suka bace, an saye manyan bindigogi masu harbor jirgin sama guda 21, sai dai guda daya kacal aka samu gani a wajen su. Yanzu haka dai cikin makonni uku da suka wuce, an fara binciken wasu manyan ofisoshin Sojojin guda 16.
Har wa yau dai ana kuma gudanar da binciken yadda aka wasu tsofaffin Sojojin suka karkatar da kudin yaki da Kungiyar Boko Haram. Cikin wadanda ake tuhuma, akwai Alex Badeh, wani babban Janar, kuma tsohon shugaban hafsin sojin kasar.
The post Wasu Sojoji na sayar da makamai ga ‘yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
