Gwamnatin Jihar Kogi za ta aro $12m domin sayen motoci
– Gwamnatin Jihar Kogi na shirin ciwo bashin motoci har guda 109 domin Kwamishinoni, ‘yan majalisu, Shugabannin kananan Hukumomi da kuma sarakunan jihar Kogi
– Gwamnatin Jihar za ta aro makudan kudi har Dala Miliyan $12 wajen sayen wadannan motoci yayin da ake fama da matsalar tattali
– Bincike ya nuna Gwamnatin Jihar Kogi na shirin sayo Motoci fiye da 100, da suka hada da; Toyota Prado kirar Jeep guda 55, da Motar Toyoto Camry guda 29, da kuma Toyoto Corolla guda 11, da ma kuma wasu Jeep din kirar Land Cruiser sababbin yayi har guda 14
Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello na ta motoci ana fama da rashin kudi.
Gwamnatin Jihar Kogi karkashin Gwamna Yahaya Bello na shirin kara jefa Jihar cikin wani sabon bashi, Gwamnan na shirin sayen motoci har guda 109 domin rabawa sarakunan gargajiya, ‘yan Majlisun Jihar, da kuma kwamishinoni, da kantomomi. Wadannan motoci dai za su kai har dala miliyan 12.
KU KARANTA: Jihar Sokoto a maido Daliban daje gida saboda rashin kudi
NAIJ.com ta samu ganin takardun, wanda Kwamishinan Kudi na Jihar, Asiru Idris, ya sanyawa hannu tun a watan Yuni. Gwamnatin Jihar za ta karbi aron kudin ne daga Zenith bank da kuma ribar kashi 8%, wanda za a biya cikin shekaru 3 masu zuwa. Binciken ya nuna cewa za a sayi motoci kirar jeep na Prado har guda 55, da kuma Toyoto Camry guda 29, sai wata Toyoto Corolla guda 11 da kuma wasu Jeep din kirar Land Cruiser ta yayin 2016.
Za dai a kashe makudan kudi har Naira N2,899,000,000 wajen sayen wadannan motoci. Inda Motocin Camry za su ci Miliyan N143million (Miliyan 13 kowace); Za kuma a kashe Miliyan dari biyar Wajen sayen Motocin Camry (Za a saye kowace akan N19m); Toyota Prado VXL guda 55 za su ci Naira Biliyan 1 da Miliyan 650. Sauran motocin za a saye su ne a kan Miliyan 315 da kuma Miliyan 240.
The post Gwamnatin Jihar Kogi za ta aro $12m domin sayen motoci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.