Najeriya ta fi Kasar Kenya nesa ba kusa ba- Femi Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode yace wanda Najeriya ta fi kasar Kenya nesa ba kusa ba.
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode, yace Najeriya fa ba sa’ar Kenya ba je. Ministan ya bada wannan bayani ne ta shafin sa na sada zumuntar zamani na Twitter.
Mista Femi Fani-Kayode ya kare Najeriya, yace Kasar Kenya tana bayan Najeriya a kowane fanni.
Femi Fani-Kayode yayi amfani da shafin sa na Twitter mai lambar @realffk, a ranar Lahadin nan inda yace Kasar Kenya ta daina ja da Najeriya. Fani-Kayode yace dole fa kowa ya san matsayin sa, duk lalecewar goma ta fi biyu. Femi Fani-Kayode yace fa duk bacin dan Najeriya to ya fad an Kenya, ko da kuwa Saraki ne.
An dai fara wannan takun-saka ne tsakanin Kasashen biyu bayan da Mark, mai kamfanin Facebook ya kawo ziyara Kasar ta Najeriya, daga nan kuma ya wuce Kenya. Abin dai ya fara ne a Ranar Juma’a nan, bayan da wata ‘yar Najeriya ta saka wani hoton Mista Zuckerberg yana cin abinci, ta kuma ce a Kasar Najeriya abin ya faru. Tuni ‘yan Kasar Kenya suka far mata, har ya kai ta bada hakuri.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yaba da halin Zuckerberg
Sai dai a wajen irin su Fani-Kayode, abin bai tsaya nan ba, yayi amfani da shafin sa wajen maida martani. Ga wasu daga cikin bayanan nasa:
Maganar gaskiya ita ce, Najeriya ta fi karfin Kenya. Ni na san tarihin Kasar su, ciki da waje. Kenya ba sa’ar Najeriya ba ce.
— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016
Lokacin da ‘Yan Kasar Kenya suke cin junan su, lokacin mu muna Jami’o’in Oxford da kuma Cambridge
— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016
Mutanen Kasar Kenya su shafa mana lafiya, dole su san cewa komai lacewar dan Najeriya, ya fi karfin da Kenya, kowane ne shi kuwa.
— Femi Olu-Kayode(FFK) (@realFFK) Satumba 3, 2016
The post Najeriya ta fi Kasar Kenya nesa ba kusa ba- Femi Fani-Kayode appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
