Nnamdi Kanu zai wargaza Najeriya
– Nnamdi Kanu ya sha alwashin tarwatsa Najeriya da kalaman gaskiya
– An dai garkame Shugaban Kungiyar ‘IPOB’ ta Biafra tun a shekarar bara
– Kanu yace tursasa masu aka yi, har ya kai suna neman Kasar kan su ta Biafra
Shugaban kungiyar ‘Indigenous People of Biafra’ Watau (IPOB) ta Biafra Nnamdi Kanu, yace zai rikita Najeriya.
Kanu, Shugaban Kungiyar mai neman ‘yancin kan Kasar Biafra,na dai daure tun shekarar 2015. Ya kuma sha alwashin rikita Kasar nan, amma fa ba da bakin bindiga ba, sai dai fatun baki. Majiyar ta rahoto cewa Nnamdi Kanu zai fallasa kwan Najeriya ga duniya.
KU KARANTA: Yan Sanda za su shiga kafar wando daya da barayi
Jaridar Nigerian Bulletin ta rahoto ta bakin mai-magana da bakin Kungiyar IPOB Emma Powerful cewa Nnamdi Kanu zai tarwatsa Najeriya. Nnamdi Kanu zai bayyanawa duniya gaskiya game da sha’anin Kasar. Nnamdi Kanu ya bayyana hada Kasar da Turawa mulkin mallaka suka yi ta zama daya a shekarar 1914 a matsayin wani abu da ba zai iya cigaba da aiki ba, don haka suke neman Kasar kan su ta Biafra.
Nnamdi Kanu wanda shine Darekta na Gidan Rediyon na Biafra yace zai cirewa Najeriyar zani a kasuwar duniya. Kanu ya sha alwashin bayyanawa iyayen gidan Najeriyar, Turawa, da ma duk wasu masana ilmin siyasa a duniya gaskiyar lamarin Najeriya. Shugaban Kungiyar ta Biafra, Nnamdi Kanu yace Kasar ta dunkule ne kurum ba don Ubangiji ya hallice ta day aba, sai dai don burin Turawan mallaka ne hakan.
Kwanan ne dai Kungiyar ta IPOB ta samu rabuwa gidaje da dama, amma wasu mata da samarin Kungiyar sun bayyana cewa babu rabuwar kai a Kungiyar ta su. A cewar su, babu wata Baraka a IPOB. Wasu daga cikin ‘yan Kungiyar, musamman; samari, ‘yan mata, dalibai da ‘yan kasuwa suna ganin dai Nnamdi Kanu wani jan gwarzo ne mai shirin karbo masu ‘yancin su, don haka da dama suka mara masa baya.
The post Nnamdi Kanu zai wargaza Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.