Abun tausayi wani mutumi ya mutu a lokacin da yake aikata wannan (Hotuna)
– Wani mutumi ya rasa ransa a lokacin da yake kokarin kama wani direban bas da ya doki motarsa
– A cewar wani mai amfani da shafin sadarwan Facebook Ola Taiwo, wani mutumi dake hanyar sa ta zuwa gurin aiki mai samu damar kai wa gurin aikin ba bayan wani hukunci mai haifar da nadama da ya yanke
An rahoto cewa mutumin yana gudu ne domin ya cimma wani diran bas, wanda ya lotsa masa motarsa ya kuma yi kokarin guduwa. Cikin fushi, murigayin ya cire takalmansa sannan ya ci gaba da bin motar dake kokarin guduwa, wannan hukuncin da ya bi ne yayi sanadiyar mutuwarsa.
KU KARANTA KUMA: Duk lalacewar gwamnan APC yafi gwamnan PDP- Danjuma
Ga abunda ya faru a cewar wanda abun ya afku a kan idanuwan sa, Taiwo:
“Wannan mutumin ya mutu a safiyar yau a tashar Onigbongbo dake Maryland, wani motar bas (danfo) ya gogi motarsa, wannan ne yasa mutumin ya bar motarsa, ya cice takalman sa sannan ya kuma bi motar danfo din da gudu, yayi kokarin kama motar amma yaron motar ya ture shi, sannan wani motar bas dake zuwa ya take kan sa, wannan ne karshen sa. Ku kalli mutumin a kwance a kasa kuma motar san a kusa dashi, ya tafi ya bar komai, dan Allah ku koyi yanda ake bin rayuwa a sannu, ya kasance Manajan Darakta (MD) a daya daga cikin fishin dake kusa.”
Dubi hotuna a kasa:
The post Abun tausayi wani mutumi ya mutu a lokacin da yake aikata wannan (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.