Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Сентябрь
2016

Wasanni: Karanta jerin kasashen da zasu buga gasar cin kofin Afirka 2017

0

A ranar Lahadi aka kammala wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Gabon za ta karbi bakunci a 2017, kuma tuni aka samu kasashe 16 da za su kara a gasar.

Kasashen sun hada da Algeria da Burkina Faso da Kamaru da Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Congo da Masar da Ghana da Guinea Bissau.

Sauran kasashen sun hada da Mali da Morocco da Senegal da Togo da Tunisia da Uganda da Zimbabwe da mai masaukin baki Gabon.

Uganda wadda ta yi ta biyu a rukuni na hudu da maki 13 da Togo wadda ta hada maki 11 a rukuni na daya a mataki na biyu, sune suka cike gurbi.

Guinea-Bissau ce kasar da za ta fara halartar gasar kofin Afirka a karon farko, yayin da Senegal ce wadda ta lashe dukkan wasannin neman shiga kofin na Afirka.

Za a fara yin gasar kofin Afirka a ranar 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun 2017.

The post Wasanni: Karanta jerin kasashen da zasu buga gasar cin kofin Afirka 2017 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса