Empress Njamah ta zama ma’aikaciyar yan sanda
Sananniyar jarumar yar wasan Nollywood Empress Njamah, an ganta cikin kayan aikin yan sanda, a inda jama’a suka shiga damuwa tare d zullumi na tunanin ko jarumar ta ajiye harkar wasan nata ta koma aikin dan sanda
Da take magana da Naij.com, sanarniyar jarumar ta bayyana cewar tananan daram a aikinta na wasan, kuma bata da niyyar barin aikin nan gaba inji Empress Njamah;
“Nasa kayan aikin yan sanda a wasan FIM din “Black Widow” ba abu mai mai sauki bane ka fito a irin wannan aikin a wasa, saboda haka nayi gwaji sosai kafin nayi abinda akeso, amman duk da haka na samu nishadi”.
Haka kuma, acikin yan wasan da mukayi wasan tare akwai, Linda Ejiafor, Daniel K. Daniel, Femi Bamigbola da kuma Chibuike Ibe wanda shiya bada umarni a wasan.
Tayi kyaufa!
The post Empress Njamah ta zama ma’aikaciyar yan sanda appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
