‘Yan Najeriya da kamfanonin kasa da kasa na kokawa yayinda matsin tattalin arziki ke addabar hada-hada
Anga ma’aikatan kampanin da yake na biyu da girma cikin hada-hadar zurga-zurgar sufurin jiragen sama a Najeriya Aero Contractors, da fuskokinsu a murtuke ranar Laraba 31 ga Agusta yayin da hukumar kampanin ta dakatarda ayyukanta ba tare da sanin ma’aikatan ba.
A tashar jirgin sama ta Asaba inda kampanin ke daukar matafiya zuwa Lagos da Abuja, anga ma’aikatan na kauda duk wani abinda keda alaka da Aero Contractors suna sawa a ofisoshinsu dake filin jirgin saman. Yanayin bashi da dadi yayin da abokai ke tausaya masu yayin da suke fita daga filin jiragen saman . An kiyasta cewa dakatarda ayyukan kampanin ya shafi fiye da ma’aikata 1000 a duka kasar da suka rasa ayyukansu. Dama kafin dakatarda ayyukan nasu, kampanin ya rage ma’aikatansa zuwa rabi .
Baya ga Aero Contractors, ana zaton wasu kapanonin sufurin jiragen sama zasu dakatar da nasu hada-hadar kafin karshen shekara dalilin matsin tattalin arziki, rashin kyawun shirin kasuwanci, manyan basussuka da kuma rashin tallafi daga bankuna. Wata majiya na fadin asarar da kapanin yayi ta kai N20billion.
Ba ayi awa 24 da tsayawar Aero Contractors ba sai kuma wani kampanin jiragen sama mai suna First Nation Airlines ta dakatarda ayyukanta. Ana zaton yin hakan kan bukatar kampanin na gyaran jiragenshi. Hukumar sa ido kan harkokin sufurin jiragen sama koko National Civil Aviation Authority, (NCAA) ta musanta kalaman da akeyi cewa kamfanonin jiragen sama na durkushewa a Najeriya duk da tsayawar kapanin First Nation.
KU KARANTA : Shehu Sani na kira ga Buhari da ya dau mataki ta gaggawa
Yawan kampanonin jiragen sama ya ragu da kashi 60 cikin shekaru goma da suka wuce. Bincike ya nuna cewa akwai matuka jiragen sama fiye da 600 masu takardar sheda wadanda basu da ayyukan yi.
The post ‘Yan Najeriya da kamfanonin kasa da kasa na kokawa yayinda matsin tattalin arziki ke addabar hada-hada appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.