-Sanata Ike Ekweremadu yayi kira ga jihohi da gwamnatin tarayya da suyi dokoki da zasu maida kiwon shanu na killataccen wurin kiwo na zamani da hukumar kiyaye dokar kiwon
-Yana cewa idan ba’a sake tsarin kasar, wanda zai kara habakarta ba to ba za’a sami mafita daga matsalolin tsaro ba.
Sanata Ike Ekweremadu, mataimakin shugaban majalisar dattawa yayi kira ga gwamnatocin jihohi dana tarayya da suyi dokoki wadanda zasu takaita kiwon shanu ga killatattun wuraren kiwo na zamani tare da hukumar da zata sa ido kan dokokin.
Mr Ekweremadu yayi wannan jawabi ne a New York ta kasar Amurka a bukin ranar Igbo na duniya koko 2016 Convention of the World Igbo Congress (WIC) inda yake cewa in ba’a sake tsarin kasar ba, to ba za’a sami cigaba ba wajen fita daga kangin tsaro, fatara da rashin cigaba ba.
“Ya kamata gwamnatocin jihohin kasashen Igbo da kuma sauran jihohin kasar su kafa doka ba tare da bata lokaci ba wanda zai takaita kiwon shanu zuwa ga killatattun wurare na kiwo irin na zamani kamar yadda kasashen da suka cigaba keyi. Bisa gaskiya, gwamnatocinmu na iya kafa wuraren, su gyara su, su kuma badasu haya. Wannan zai sa bisashen suyi lafiya, a sami amfani mai kyau, aikin yi, kyakyawan zamantakewa a kuma bambanta barayi da ‘yan ta’adda daga masu kiwon gaskiya” a cewarsa. Ya kara da cewa bai kamata gudanar da dokar ya zama hannun hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya kadai ba.”
“Abin ban takaici da damuwa, shine idan kayi dokar kamar yadda jihar Ekiti tayi, dole ka dogara kan hukumomin tsaron da aka sani wajen tafiyarda dokar. Ya kamata gwamnatocin jihohi su dauki matakin ganin dokar ta bada izinin kafa hukumar tsare dokar kamar gandurobobin daji wadanda zasu zagaye dazuzzukan domin ganin an tafiyar da dokar na kama masu laifi da kuma hukuntasu yadda zai zama sharadi ga wasu”.
Ya dora laifi kan “gwamnatocin sojoji da akayi a baya da laifin bata tsarin kasa wanda magabatanmu suka bar mana a tarurrukan kundin tsarin mulkin kasa a matsayin hadin kan kasa.”
Настройки GameHub и Winlator для игры в Prey (2017) на Android
The dairy industry would like Gen Z to drink more milk, so they made a Fortnite diner tycoon game
Microsoft warns of 'active attacks' on its government and business server tech, with one cybersecurity expert claiming that they should 'assume that you have been compromised'
'I destroyed months of your work in seconds' says AI coding tool after deleting a devs entire database during a code freeze: 'I panicked instead of thinking'