-Tsagerun Neja Delta a Najeria sun gaya ma mazauna kusa da cibiyoyin mai da iskar gas a yankin suyi saurin kauracewa kada tsagerancin ya shafesu
-Niger Delta Greenland Justice Mandate (NDGJM) tace an dana ma wasu cibiyoyi nakiyoyi ana jiran tadasu
Akwai yaki bada dadewa ba a yankin Neja Delta kuma tsagerun yankin sun bukaci mazauna kusa da cibiyoyin mai da iskar gas a yankin su gaggauta kauracema wuraren domin kada tsagerancin ya shafesu. Yayin da suke bada sanarwar, Niger Delta Greenland Justice Mandate (NDGJM) tace an dana nakiyoyi ga wasu cibiyoyi ana jiran tayar dasu, tana mai cewa dalilin rashin tayarwar shine mutanen dake kusa da cibiyoyin.
“Muna kara gargadi da kuma rokon mazauna kusa da cibiyoyin mai da iskar gas a yankinmu da suyi saurin yin kaura daga yankin. “Wannan gargadi ya zama dole domin bama son abin ya shafi jama’ar da dominta muke yin wannan shahadar . An dana nakiyoyi a wasu wurare muhimmai domin fasa su. Abinda ke dakatar damu shine kasancewar mutane dake kusa. Ba zamu daina wannan gwagarmayar ba sai abokan gabarmu Najeriya ta yarda da abinda ya kamata” cewar jawabi daga bakin mai magana da yawun kungiyar Aldo Agbalaja.”
NDGJM ta gargadi gwamnatin tarayya da tayi hankali da Chief Edwin Clark, tana cewa dakatarda bude wuta da dattijon ya ambata mamadin tsagerun karya ce tsagwaronta.
“Duk wannan kiraye-kirayen da akeyi, neman kudi ne kawai, kamar taron da Clark ya kira ne wanda ke cike da ‘yan Ijaw a garin Effurun, domin nunama gwamnati suna aikin kudin da suka amsa. Kwamandojin Niger Delta Greenland Justice Mandate na gayama duniya kada a yarda da wannan yaudarar. Muna da hanyar sadarwarmu, amma ba kira ba. Idan hukumomin tsaron Najeriya da gaske sukeyi na kama tsageru to su gano wadanda sukace sunyi magana da ODU tunda suna da lambarsa . Idan munyi maganarmu “mai Kara” ta gaba to sai su kama ODU wanda ke kiran kansa shugaba” cewar sanarwar
A wata sanarwa da Gen. Aldo Agbalaja ya sama hannu, kungiyar na gargadin gwamnatin tarayya da tayi hankali da wasu shuwagabannin bangaren domin zakuwarsu ta samun kudi na iya sasu su damfari kowa da sunan ci gaban yankin Neja Delta.
The dairy industry would like Gen Z to drink more milk, so they made a Fortnite diner tycoon game
Настройки GameHub и Winlator для игры в Prey (2017) на Android
'I destroyed months of your work in seconds' says AI coding tool after deleting a devs entire database during a code freeze: 'I panicked instead of thinking'
Краткая биографическая справка о центральных персонажах Mafia: The Old Country