Buhari ya yi maraba da gano ma’adinin Nickel
An sanar da shugaba Muhammadu Buhari a hukumance samun karfen Nickel da aka yi a karkashin kasa a jihar Kaduna
A wani hoto da Babban mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Femi Adesina ya yada, an gabatarwa da shugaban kasa taswirar wurin da ka gano ma’adinin karfen Nickel da ka aka gano a arewacin kasar.
Ministocin biyu a lokacin da suke gabatarwa da shugaban kasa taswirar inda aka gano ma’adinin karfen Nickel a arewacin kasar
A hoton, an ga Ministan kula da wuraren hakar albarkatun karkashin kasa da bunkasa karafa, Dakta Kayode Fayemi, tare da karamin Minista a Ma’aikatar Abubakar Bawa Bwari, na nunawa shugaba Buhari taswirar wurin da aka gano ma’adinin karfen mai matukar daraja, a fadar shugaban kasar.
KU KARANTA KUMA: Gano sinadarin Nickel zai habaka ci gaba a ma’aikata
Labarin gabatarwa Shugaban kasa labarin gano karfen, ta hanyar gabatar masa da taswirar wurin, na fitowa ne bayan da wani dan jarida Ja’afar Ja’afar, ya yada hoton da abokinsa Rufa’I Dabo ya saka a shafin sada zumunta da muhawara na Facebook, bayan da ya ziyarci kananan hukumomin Shanonon da Bagwai a Kano.
Dangane da hoton Rafa’i ya bayyana cewa, a kauyukan akwai wadataccen zinare da sauran ma’adinai a karkashin kasa, a inda ba a bukatar manya-manyan injina domin hako su, saboda a cewarsa, mutanen wurin da ba sa wahalar da kansu wurin hakar ‘yan ramuka domin tono su.
Idan za a tuna, wani Kamfanin Australia ya shaidawa jaridar kasar cewa, ya gano ma’adinin Nickel mai matukar daraja a duniya a kauyen Dangoma a arewacin jihar Kaduna, wanda hakan a cewar masana, zai sa kasar ta samu ci gaban tattalin arziki.
The post Buhari ya yi maraba da gano ma’adinin Nickel appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.