Wani dalibi mai bautan kasa ya nutse cikin rafi a jihar Ribas
Wani dalibi mai bautan kasa wanda aka fi sani da NYSC, ya rasa rayuwar sanadiyar nutsewa a ruwa,kuma an birne shi.
Game da cewar wani abokin shi wanda ya bayyana yadda akayi, dalibin mai suna Dayo ya bakunci lahira ne yayinda ta tuntsuro daga cikin kwale-kwale.
An bada rahoton mutuwarsa ne a ranan 27 ga watan agusta. Yaje aski ne a shagon wanzami yayinda ya nutse cikin ruwan. Bayan kwanaki 2 aka ga gawar sa kuma aka birne shi a ranar Juma’a ,2 ga watan Satumba.
Wani abokinsa yace :
“Corper dayo wani mai fara’a ne. kuma yana yin ibada.mu masu bautan kasan Isaka,fatakwal muna mika ta’aziyar mu ga abokinmu wanda ya rasa rayuwarsa.
Corper dayo ya tsallaka rafin ne domin ya je yayi aski saboda shirin ranan lahadi amma bai dawo ba baya y agama aski a shagon wanzamin saboda lokacin da ya kai rafin,ya zame daga cikin kwale-kwalen yayinda yake kokarin zuwa inda muke zama. Mun yi juyayi muna rokon Allah yasa a ceto ransa yayinda aka shiga neman sa a cikin rafin.
KU KARANTA : Jami’in soja ya bayyana sirrin Boko Haram
Abun takaici , an ganshi kwanaki biyu baya a saman ruwa. An birne shi ranan 2 ga watan satuma. Ina son inyi amfani da wannan daman cewa duka masu bautan kasan da ke zaune a irin wannan yankin suyi a hankali kuma su dinga sanya kayan rafi komin karantan ruwan.”
The post Wani dalibi mai bautan kasa ya nutse cikin rafi a jihar Ribas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
