Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Сентябрь
2016

Zaben jihar Edo: PDP na zargin INEC da son kai

0

– Jam’iyyar adawa ta PDP ta kai kuka akan zancen cewa Hukumar INEC na bauwa APC fifiko wajen shirye shiryen zaben da za’a gudanar ranan 10 ga watan Satumba

– Jam’iyyar tace ta nemi Hukumar INEC ta bada wasu labarai da ta baiea jam’iyyar APC amma har yanzu ba’a basu ba

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Edo ta kawo zargin cewa Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC na hada baki da jam’iyyar APC bisa ga zaben jihar da za’a gudanar ranan 10 ga watan Satumba.

Game da cewar Jaridar Daily Post, PDP na tuhumar INEC ns baiwa APC wasu sirrin da zai iya bata nasara a zaben da za’a gudanar a karshen makon. Saboda ayi daidai, PDP ta nemi ita ma a bata sunayen Wadanda zasu gudanar da zaben jihar.

A wata wasikar da kakakin jam’iyyar PDPChris O Nehikhare, ya bada , yace : “A cikin shirye shiryen mu na zaben gwamnan jihar Edo da za’a gudanar ranan 10 ga watan satumba, mun nemi ganawa da ma’aikatan INEC da zasu gudanar da zaben jihar Edo. Amma har yau 5 ga watan satumba, ba’a bayyana sunayen su ba. Labarin da muka samu shine INEC ta baiwa jam’iyyar APC daman ganawa da ma’aikatan da muka nema muma a bamu. Munada masaniya cewan an baiwa APC daman shiga yanar gizon INEC da kuma yadda suke tattara kuri’u ta yanar gizo.

“Muna sane cewa an yi hakan ne domin a baiwa wasu ma’aikatan INEC daman canza kuri’u a wuraren suke shan kasa a ranan zabe ko kuma su tayar da tarzoma a wuranren. Muna sa ran cewa irin wannan ganawar idan aka bamu, zamu iya gabatar da irin wadannan koke-koken.

KU KARANTA: Najeriya na jiran Ndigbos – Okorocha

A bangare guda Dakta Segun Abraham, wanda ya sha kasa a zaben share fagen jam’iyyar APC a jihar ondo ya dau na annabawa akan sakamakon zaben, yayinda ya taya zakaran zaben , Rotimi Akeredolu muran. A wata sako da ya bayar a ranan lahadi, 4 ga watan satumbaa babban birnin jihar Akure, Abraham ya taya Akeredolu ,wanda ya lashe zaben murna . Jaridar Sun ta bada rahoto.

The post Zaben jihar Edo: PDP na zargin INEC da son kai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса