Olusegun Abraham ya taya Akeredolu murna
–Abraham ya taya Akeredolu murna duk da ya kayar da shi a zaben fidda gwanin APC.
–Akeredolu ya lashe zaben firamaren da da kuri’u 669,yayinda Abraham ya zo na biyu da kuru’u 635
–Oke da Boroffice sun zo na 3 da 4
Dakta Segun Abraham, wanda ya sha kasa a zaben share fagen jam’iyyar APC a jihar ondo ya dau na annabawa akan sakamakon zaben.
A wata sako da ya bayar a ranan lahadi, 4 ga watan satumbaa babban birnin jihar Akure, Abraham ya taya Akeredolu ,wanda ya lashe zaben murna . Jaridar Sun ta bada rahoto.
Yace : “Ina taya Akeredolu, wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar mu mai girma,APC a jihar ondo. Godiya ta musamman zuwa ga gwamnan jihar jigawa,Alhaji Badaru Abubakar tare da tawagarsa Wadanda suka tabbatar da cewa an gudanar da zaben jihar ondo cikin zaman lafiya da lumana.”
Abraham ya gode wa magoya bayansa kuma yace duk da ya sha kasa, zai cigaba da biyayya ga jam’iyyar. Yace : “Ina mika godiya ta ga masoyan mu domin goyon bayan da suka bada tun lokacin yakin neman zaben har yau. Na san ran ku a bace yake. Kun yi kokarin shiga lungu da sako domin bayyana aniyar mu.Ina rokon ubangiji ya kawo cigaban da muke so a jihar ondo.”
“Ba zan juya bayana ga mutanen jihar ondo ba. Zan cigaba da bada gudunmuwats domin kawo cigaba Jihar. Akeredolu ya lashe zaben firamaren da da kuri’u 669,yayinda Abraham ya zo na biyu da kuru’u 635.”
KU KARANTA: Onuesoke ya caccaki gwamna Masari domin sukar Jonathan
Mutane 24 ne sukayi takara a zaben. Ga sakamakon zaben: Olusola Oke – 576 , Ajayi Borrofice- 471 ,Tayo Alasoadura- 206 , Bode Ayorinde- 67 , Jumoke- Ajasin Anifowose- 1, Tunji Ariyomo- 2, Tunji Abayomi- 5, Afemi Mayowa- 13 , Adegbomire Adebiyi- 8 , Adekunle Adekunle- 8, Ayo Akinyelure- 3 ,Jamiu Afolabi, 44 , Ademola Adegoroye- 0 , Bukola Adetula – 8, Foluso Adefemi – 13 , Victor Olabimtan- 18 da Boye Oyewumi – 7. Mutanen 2774 ne sukayi zaben da Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC ta shaida.
The post Olusegun Abraham ya taya Akeredolu murna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.