Yan daba sun kashe wani tela a jihar Legas
– Wasu yan daba sun kashe tela a unguwan ikorordun jihar Legas
– Mutumin mai suna Mr Segun Showemimo,tela ne kuma mai yara 2
– Kakakin jami’an yan sandan jihar Dolapo Badmus ta tabbatar da labarin a ranan litini 17 ga watan oktoba
Yan daba a legas
Wata tashin hankali ta faru a ikorodu karshen makon nan inda yan daba suka kashe wani tela kuma suka fara jifan gawarsa.
An kashe Mr Segun Showemimo,ne a shagonsa dake Lemo,ikorodu aranan asabar da rana.
Yan daban su kimanin 4 sanya da kaya iri daya sun far ma unguwar kan Babura 2 suna harbi sama domin tsorata jama’a.
KU KARANTA:Gwamnati ta bada Ranar Alhamis a matsayin hutu
Wani marufu,dan uwan wanda aka kashe yace sun jefe shi bayan kisan , yayi bayani : daki nan a kusa da shagon dan uwana. Abunda yafi bani mamaki shine bayan sun harbe shi a kiri da kai ,sai suka fito da dutsuna daga cikin leda suna jifan gawarsa. Suna rawa suna zagaye gawar kafin suka tafi. Bamu san dalilin kisan sa basa saboda mutum ne mai saukin kai.
Kakakin jami’an yan sandan jihar Dolapo Badmus ta tabbatar da labarin a ranan litini 17 ga watan oktoba. Kuma tace ana gudanar da bincike cikin al’amarin.
The post Yan daba sun kashe wani tela a jihar Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.