Obanikoro ya fasa kwai, ya jefa Fayose cikin matsala
– Musliu Obanikoro ya fasa kwan yadda ya raba N4.7b da ake zargin ya sace
– Sai dai yace an raba wannan kudi ne domin kawar da Kungiyar Boko Haram daga Legas
– Obanikoro yace ta jirgin sama aka tura kudin
Sanata Musiliu Obanikoro
Kamar dai yadda aka sani Tsohon Karamin Ministan tsaro lokacin Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan, Musliu Obanikoro ya dawo Najeriya, inda har ya sallama kan sa ga Hukumar EFCC. Sai dai Tsohon Ministan, Musliu Obanikoro ya tsoma Gwamna Fayose na Jihar Ekiti cikin babbar matsala.
Ana zargin Musliu Obanikoro da shan kwana da wasu kudi da suka kai Biliyan hudu da miliyan dari bakwai da hamsin da biyar ta wani Kamfanin sa mai suna Slyva Mcnamara. Wadannan kudi dai sun fito ne daga Ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro ONSA a lokacin. Sai dai Obanikoro yace an raba wannan kudi ne domin yakar da ‘Yan Kungiyar Boko Haram da ke Jihar Legas
KU KARANTA: Fayose ne babban dan adawan Buhari
Musliu Obanikoro yace ya turawa Ayo Fayose Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyu da ashirin da uku da kuma wasu Biliyan daya da miliyan dari uku cikin kudin ta hannun wani wai shi Mista Abiodu Agbele. An dai tura wannan kudi ne ta jirgin sama.
Wadannan kudi dai duk suna cikin Dala Biliyan biyun da aka yi awon gaba da su daga Ofishin ONSA na Kasa, watau mai bada shawara kan harkar tsaro, Sambo Dasuki, a lokacin. Wadannan kudi dai asali na sayan makamai ne.
The post Obanikoro ya fasa kwai, ya jefa Fayose cikin matsala appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.