Kasafin Kudi: Kwanan nan Hukumar EFCC za ta nemi Dogara
– Hukumar EFCC ta damki wasu manyan ma’aikata game da badakalar kasafin kudin bana
– Watakila kwanan nan Hukumar EFCC za ta bi ta kan Yakubu Dogara
– Ana zargin badakala a cikin kasafin kudin Kasa da Majalisa ta amince da shi
Jami’an hukumar EFCC
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa na cigaba da binciken zargin badakalar kasafin kudi na bana. Yanzu haka Jaridar Punch ta bayyana cewa an kama wasu manyan ma’aikata har 16 daga wasu Ma’aikatun Kasar game da batun da ya shafi kasafin kudi na wannan shekarar.
Wani babban Jami’in Hukumar EFCC ya shaida haka, yace tabbas ana ta bincike a hankali. Hon. AbdulMumin Jibrin wanda shine Tsohon Shugaban Kwamitin kasafi a Majalisar ya rubuta wasika ga Hukumar EFCC inda yake zargin Shugaban Majalisar da wasu da karkatar da wasu Naira Biliyan arbain daga Kasafin Kudi na bana.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama Murtala Nyako
Majiyar mu sun nuna cewa yanzu haka EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Kasar tana binciken Shugaban Majalisar Kasar Yakubu Dogara da sauran manyan ‘Yan Majalisar. Yace ana ta binciken a hankali kuma kwanan nan za a nemi shi Dogara Yakubu domin yayi bayani.
Sakataren kwamitin na PACAC, Farfesa Owasanoye yace sun zauna da shi Tsohon Shugaban Kwamitin kasafi na Majalisar wakilai AbdulMumin Jibrin, kuma sun ba Shugaban Kasa shawarar abin da ya dace. Tuni ma dai an kama ma’aikata kusan fiye 180 da laifin sauya abin da ke cikin kasafin kudin Kasar.
The post Kasafin Kudi: Kwanan nan Hukumar EFCC za ta nemi Dogara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.